Pages

Games

Sunday 8 October 2017

Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna

Ana zargin wani jami’in dan sanda a jihar Kaduna da harbin wata budurwa saboda taki amince da soyayyarsa
- Buduruwar ta kasance daga kauyen Gadar Mallam mamman dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja
- Sha’awa ta bayyana cewa dan sandan ya labe ne a lokacin da ya harbe ta
Ana zargin wani jami'in dan sanda a Kaduna da harbin wata budurwa da bindiga saboda taki amincewa da soyayyarsa.
Majiyar bestarewa.com.ng
 ta ruwaito budurwar mai suna Sha’awa Nasiru, mai kimanin shekaru 20 da haihuwa daga kauyen Gadar Mallam mamman dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Majiyar ta bayyana cewa dan sandan ya labe ne a lokacin da ya hangi sha’awa ta shiga wani gida, yayin da take fitowa sai ya kira sunanta, tana amsawa zai ya saka mata harsashi.

KarkYi share wannan
Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna
Budurwar da aka harbe a kan so

KarkYi share wannan
Nan da nan mutane suka watse a guje sakamakon jin harbin bindigar kafin daga bisani wasu suka garzaya inda budurwar take a kwance cikin jini suka dauke ta zuwa asibitin Doka dake jihar Kaduna, amma abin yafi karfinsu, inda suka ce a mika ta zuwa babban asibiti, sai dai hakan bata samu ba sabida yajin aikin da kungiyoyin ma’aikatan lafiya suke yi, ciki kuwa har da asibitin koyarwa dake Gwagwalada.

KarkYi share wannan
Wata kawar ta mai suna Salamatu Sani ce ta shaidawa wa majiyar mu cewa, “Sha’awa ta shaida wanda ya harbe ta a lokacin da suka iso wajenta cikin gaggawa, a inda ta shaida cewar ‘insfekto ne' ", inji kawar ta.

KarkYi share wannan
Sai dai duk yunkurin da majiyar tamu tayi don jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu abun yaci tura domin yaki amsa kiran kuma yaki maido da sakon tes da akayi masa kan batun.

KarkYi share wannan

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie