Pages

Games

Tuesday 23 August 2016

Ko kun san sau nawa aka kashe Shekau?


Kan kungiyar ta Boko Haram ya rabu gida biyu

Rundunar sojin Najeriya ta fitar sanarwar cewa ta yi wa shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, mummunan rauni a ranar juma'ar da ta gabata, amma ko kun san sau nawa aka ta yi ikirarin kashe shi a baya?
  • A shekarar 2009 rundunar sojin Najeriya ta sanar da mutuwar shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, amma ba a shekara ba, Shekau ya bayyana a wani faifan bidiyo.
  • A shekarar 2013 rundunar hadin gwiwa ta JTF ta bayyana cewa dakarunta sun harbi Shekau kuma sun yi masa mummunan rauni, lamarin da ya sa aka tsallaka bakin iyaka da shi zuwa garin Amchide da ke kasar Kamaru
  • Kakakin rundunar JTF na wancan lokacin, Kanar Sagir Musa, ya ce sun samu bayanan sirri da suka nuna musu cewa Shekau ya mutu, a tsakanin ranar 25 ga watan Yuli zuwa ranar 3 ga watan Agustan 2013.
  • Sai dai a ranar 13 ga watan Agustan ne kuma Shekau ya kara bayyana a wani faifan bidiyo, abin da JTF ta yi watsi da shi da cewa yaudara ce kawai.
  • Haka kuma a shekarar 2014 dakarun Najeriya sun yi ikirarin kashe shugaban na Boko Haram a yakin da suka fafata a garin Konduga da ke jihar Borno.
  • A wannan karon ma ba ta sauya zani ba, domin a farkon watan Oktobar 2014 ne kuma Shekau ya fito a wani faifan bidyo ya sake karyata kashe shin da aka ce an yi.
  • A cewar rundunar sojin Najeriya tuntuni suka kashe Shekau na ainihi, amma sauran mutanen sunan shugaban na Boko Haram suke amfani da shi.
Tuni masana sun fara sharhi a kan sanarwar ta jikkata shugaban na Boko Haram da sojoji suka fitar, Kabiru Adamu mai sharhi ne a kan al'amuran tsaro a Najeriya:
Read More »
Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie