Pages

Games

Showing posts with label Labarai. Show all posts
Showing posts with label Labarai. Show all posts

Thursday, 26 April 2018

Labaran duniya : Hotunan mummunan hadari da ya faru a Abuja

Wata babbar motar daukar yashi ta yi mummunan hadari a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya inda ta abka ta doki fililon babbar gada a unguwar Mabushi.
Hadarin ya faru ne da yammacin Laraba a daidai lokacin da ake tashi daga aiki.
Hadarin ya shafi wasu motocin tasi guda biyu inda akalla mutane 5 suka mutu.
Rahotanni sun ce rashin birki ne ya sa babbar motar da doki ginshikan babbar gadar.
Da farko motocin tasi guda biyu ne suka fara yin hadari a kasan gadar da ke zuwa Gwarinpa.
Bayan isowar jami'an tsaro suna kokarin diba hadarin 'yan tasi, sai ga babbar motar a guje kuma a lokacin da suke kokarin tsayar da shi, rahotanni suka ce ya abka ginshikan gadar.
Wasu shaidu sun ce direban babbar motar ya yi ta yi wa jami'an tsaro hannu su kauce saboda ba ya da birki, kafin ya ci birki da ginshikan babbar gadar a Abuja.
Mutanen da ke cikin babbar motar dai babu wanda ya fita, dukkaninsu sun mutu
An shafe lokaci ana kokarin fitar da gawar yaron babbar motar da direba wadanda kan motar ya game da su a ginshikan gadar
Wannan dai wani mummunan al'amari ne da ya faru a Abuja wanda ya haifar da cunkuson mutane da ababen hawa.
Read More »

Wednesday, 25 April 2018

Labaran duniya : An gano zuciyar Sarauniyar Faransa da aka sace

'Yan sandan a Faransa sun gano wani akwatin zinari da ke dauke da zuciyar daya daga cikin wata jaruma, wadda aka sace daga wani gidan adana kayan tarihi a makon jiya.
Akwatin wanda yake dauke da kayayyaki mallakin Sarauniya Anne, an kera shi ne a karni na 16.
'Yan sanda sun kama mutanen biyu a ranar Asabar kuma sun kai su inda aka binne akwatin kusa da birnin San Nazaire da ke yammacin kasar.
Anne kadai ce macen da aka taba nada wa Sarauniyar Faransa sau biyu.
An ce tana daya daga cikin mata mafiya arziki, kuma aka fara yi wa alkawarin auren Yarima Edward na Ingila.
Me ya sa Atiku ke son shugabancin Najeriya?
'An tsinci yara 26,000 a titunan jihar Kano'
Yadda 'yan Afirka suke fama da wariyar launin fata
Amma yariman ya yi batan-dabo lokacin yana yaro, tare da dan uwansa Richard - an zargin kawunsa King Richard III da sanadiyyar bacewarsu.
Daga baya Anne ta auri 'yan gidan sarautar Faransa guda biyu, Charles VIII a 1491 sannan kuma dan uwansa Louis XII a shekarar 1498.
Akwatin zinarin yana da nauyin Gram 500 da siffar zuciya, yana kuma da rubutun tsohon harshen Faransanci a jikinsa.
Hukumomin kasar sun bukaci a dawo da akwatin, don sun yi imani da cewa barayi ba su fahimci muhimmancin tarihin zuciyar ba, wanda aka kubuta daga narkewa bayan juyin juya halin Faransa a shekarar 1789.
Read More »

Tuesday, 24 April 2018

Labaran duniya : Hisba ta tsince yara fiye da 26,000 a titunan Kano – Sheikh Daurawa

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta ce a shekara biyun da ta wuce ta tsinci yara fiye da 26,000 da ke gararamba a titunan jihar.
A cewar hukumar, galibin yaran da aka tsinta dai sun fito ne daga wasu kasashe masu makwabtaka da Najeriya da kuma jihohin kasar masu makwabtaka da jihar Kano.
Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce bai ga dalilin haihuwar 'ya'yan da ba za ka iya rike su ba.
Hakazalika malamin ya ce babu wani dalili da zai ya sa ka bar yaro kankani yana gararamba a kan titi. Ya ce laifi ne babban ka haifi mutum kuma ka jefar da shi a kan titi.Ya ce idan sun tsinci yaro ba su ne suke kula da su ba.
Ya ce suna mayar wa iyayen yaran ne kuma su ja musu kunne kan su mayar da hankali tarbiyyarsa.
"Wadanda kuma ba a samu iyayensu ba, suna ba mu wahala. Wani babu garinsu, babu cikakken bayani da zai fada maka daga ina yake."
Ya ce idan suka samu irin haka suna kai wa kwamiti da gwamnati ta kafa don kula da irin wannan hali.
Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar
Read More »

Labaran duniya : An 'kashe' mutum 18 a coci a Benue

Akalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu, bayan wani hari da aka kai wata cocin darikar katolika watau St Ignatius Catholic Church a jihar Benue kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.
Wadansu mahara ne wadanda gwamnatin jihar ta ce makiyaya ne suka kaddamar da harin a garin Ayar-Mbalom da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas.
Kuma cikin mutanen da aka kashe har da limaman coci guda biyu.
Har ila yau maharan sun kona akalla gidaje kimanin 50, a cewar gwamnatin jihar ta bakin mai magana na yawun jihar Terver Akase.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan, gami da mika jaje ga gwamnati da al'ummar jihar.
Ya ce kisan mutanen a coci "aikin shaidanci ne,kuma yunkuri ne na haddasa rikicin addini, da janyo mummunan zubar da jini."
Wata sanarwa da kakakin gwamnatin Femi Adesina ya fitar ta ce, Shugaba Buhari ya sha alwashin zakulo maharan da kuma hukunta su.
Jihar Benue jihar ta dade tana fama da rikicin makiyaya da manoma.
Read More »

Labaran duniya : Yadda dan majalisa ya rasa iyalansa 10 a rana daya

An yi jana'izar mutum goma a Zamfara, dukkaninsu iyalan wani dan majalisar dokokin jihar, wadanda suka mutu a sanadiyyar hadarin mota.
Motar da suke ciki ce ta yi taho-mu-gama da wata babbar motar dakon kaya a ranar Lahadi, yayin da suke koma wa gida daga hidimar aure.
An dai yi jana'izar mamatan a garinsu na 'Yarkufoji dake karamar hukumar Bakura.
Wakilin BBC ya ce tafiya ce ta farin ciki da neman karuwa, to amma sai kwatsam ta rikide ta koma ta rashi da matukar jimani.
Iyalan dan majalisar mai wakiltar mazabar Bakura a majalisar dokokin jihar ta Zamfara, Hon Saidu Danbala 'Yarkufoji ne dai hadain motar ya rutsa da su.
Jami'in hulda da jama'a na Majalisar dokokin jihar Zamfara, Malam Nasiru Usman Beriki, ya ce hadarin ya faru ne bayan sun isa garin Gusau domin hidimar auren daya daga cikin 'yayan Hon Saidu.
"Bisa hanyarsu ta komawa gida ne bayan sun bar Gusau, sun wuce Bungudu, sun kai gadar da ke fita garin Bungudu, suka hadu da wata babbar mota wadda ta ke dauke da kwalaben lemu", in ji shi.
"A cikin mutum goma da suka rasu, akwai 'yayansa mata uku da dan shi namiji daya, da jikokinshi uku, da dangin matarsa su biyu, da kuma direban motar"
Malam Nasiru ya ce matarsa da kuma jaririnta sun tsira .
Hatsarin mota ya hallaka mutane 18
An haifi jariri shekaru 4 bayan mutuwar iyayensa
Jami'in wayar da kan jama'a na Hukumar Kiyaye Haduran ta Kasa FRSC reshen jihar ta Zamfara, Malam Nasiru Ahmad ya shaida wa BBC cewa baya ga iyalan dan majalisar jihar da suka rasu, yaron babbar motar da suka yi karo da ita, shi ma ya rasu.
Wannan hadari dai ya kara fito da irin yadda jama'a ke rasa rayukansu a haduran mota a kasar, galibi sanadiyyar rashin kyawun hanyoyin, da tukin ganganci da gudun fiye da kima.
Read More »

Monday, 23 April 2018

Labaran duniya : Iran ta yi barazanar komawa shirinta na nukiliya

Ministan harkokin kasashen wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, ya ce kasarsa a shirye take ta sake komawa harkar nukiliya gadan-gadan idan Shugaba Trump na Amurka ya soke yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekara ta 2015.
A karkashin yarjejeniyar, Iran ta amince ta sassauta shirinta da nukiliya domin samun sassaucin takunkuman karayar tattalin arziki.
Sai dai shugaba Trump na ganin cewa akwai rashin adalci a yarjejeniyar, inda ya bayar da wa'adin zuwa ranar 12 ga watan Mayu don sake bitar yarjejeniyar.
Mista Zarif ya ce Washington na gindaya hujjojinta ne kan abin da ya shafe ta ko ribar da za ta samu.
Iran ta jaddada cewa shirinta na nukiliya ba na yaki ba ne.
Saudiya za ta kera makamin nukiliya saboda Iran
Iran ta yi barazanar yin raddi ga Amurka
An daure mace saboda bude gashinta a Iran
Read More »

Labaran duniya : Ko tiyatar kwaskwarima da ake yi wa al'aurar mace na da illa?

Gwamnatin Birtaniya ta bukaci babbar likitar gwamnatin kasar da ke aikin tiyatar gaban mace da ta bayar da sabuwar kididdiga a kan yawan matan da aka yi wa tiyata a gabansu.
Tun a shekarar 2008, aka yi wa mata dubu 27,016 irin wannan aiki na sanya musu wata raga a gabansu idan suna fama da matsalar kasa rike fitsari ko kuma idan gabansu ya dan saki domin ta taimaka musu.
To amma, kididdiga ta nuna cewa an cire wa mata 211 ragar.
Matan dai suna korafin cewa ragar da aka sanya musun tana janyo musu matsala a gaban nasu, shi ya sa suke zuwa a cire.
Yanzu dai gwamnatin Birtaniya ta bukaci da a ba ta sabuwar kididdiga a kan adadin matan da aka yi wa wannan tiyata a cikin wata guda.
Me zai sa miji ya yi wa matarsa komai a duniya?
Ana zargin R Kelly da sanya wa wata mata ciwon sanyi
Matsayin musulunci kan sanya turare a al'aurar mace
Wata sabuwar kididdiga da hukumar inshorar lafiya ta Birtaniya ta fitar, ta nuna cewa an yi wa mata 21 tiyatar cire ragar da aka sanya musu a tsakanin shekarun 2016-17, ragi a kan wadanda aka cire wa a shekarar 2015, kuma ya haura zuwa 40 a shekarun 2011-12.
A shekarar 2016-17 mata 2,680 a ka yi wa tiyatar idan aka kwatanta da mata 3,413 da a ka yi wa aiki a shekarar 2011-2012.
Ministan lafiya na kasar, Lord O'Shaughnessy, ya ce ana bukatar kididdigar ne saboda a gano adadin matan da ake yi wa irin wannan tiyata a kasar.
Ya ce, saboda muhimmancin al'amarin, aka bai wa shugabar likitocin da ke irin wannan tiyata Farfesa Dame Sally Davies, damar ta ji ra'ayoyin ma'aikatan hukumar inshorar lafiyar da kungiyar likitoci masu tiyata, da kuma kungiyar matan da aka yi wa irin tiyatar da suka samu matsala bayan aikin.
Karin bayani
An dai kiyasta cewa, an yi wa mata dubu 100 tiyata a gabansu ta hanyar sanya musu wata raga da za ta tallafawa gaban nasu a Ingila.
Mafi yawancinsu dai ba su samu wata matsala ba bayan tiyatar.
Kazalika wasu mata fiye da 800 sun dauki matakin shari'a a kan hukumar inshorar lafiya ta kasar bayan an yi musu tiyatar.
Ba kasafai ake irin wannan tiyata a wasu kasashen duniya ba, musamman kasashen Afirka, domin da yawa mutane ma ba su san ana irin tiyata ta sanya raga a gaban mace idan gaban nata ya samu matsala ba.
Me zai sa budurwa shan kayan mata?
Adikon Zamani: Illar tallace-tallacen 'yan mata
Read More »

Saturday, 21 April 2018

Labaran duniya : 'An yi wa kalaman Shugaba Buhari kan matasa mummunar fahimta'

A Najeriya, wasu mukarraban shugaban kasar sun ce an yi mummunar fahimta game da kalaman da shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa mafi yawan matasan kasar ci-ma zaune ne.
Shugaba Buhari yana magana ne a taron kasashen renon Ingila dake gudana a birnin Landan.
Sai dai kalaman sa na ci gaba da tayar da kura a tsakanin matasan kasar musamman a kafafen sada zumunta na zamani.
Matasa da dama dai sun nuna damuwarsu kan kalaman da suka ce na zubar da kima ne.
'Yan Nigeria na da gajen hakuri — Buhari
Abin da ya sa na yi wa Buhari uzuri - Soyinka
Sai dai mai bai wa shugaban shawara kan kafafen watsa labarai Sha'aban Sharada, ya ce matasa ba su fahimci kalaman Shugaba Buhari ba.
Ya ce "duk wanda ya kalli bidiyon Shugaba Muhammadu Buhari zai ga cewa ya furta kalaman ne cikin raha".
Sha'aban Sharada wanda ke cikin 'yan tawagar shugaban kasar da ke ziyara a Landan ya ce furucin da Shugaba Buhari ya yi hannunka mai sanda ne ga al'ummar kasar domin su tashi tsaye wajen neman na kansu.
Ya ce a ko wanne lokaci batun yadda za a inganta rayuwar matasa shi ne babban abun da Shugaba Buhari ya sa a gaba.
Ce-ce-ku-ce
Matasa a Najeriya sun yi ta ce-ce-ku-ce tare da mayar da martani kan kalaman Shugaba Buharin, musamman a shafuka sada zumunta.
Wasunsu sun yi ta yi wa shugaban ba'ar cewa ai matasan ne suka yi tsaiwar-daka har ya zama shugaban kasa.
To sai dai duk da haka akwai wasu matasan da suke ganin babu aibu a maganar shugaban, domin kuwa bai hada matasan ya yi musu kudin goro ba, ya dai ce da dama daga cikinsu ne suka da wannan matsala.
Haka kuma wasu na da ra'ayin cewa gaskiya ce zalla shugaban ya fada, don haka babu wani abin tada jijiyar wuya.
Read More »

Labaran duniya : Koriya ta Arewa ta dakatar da shirinta na nukiliya

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya sanar da cewa ba zai sake gwajin harba makamai masu linzami ba, kuma zai rufe tashoshin da ake gwajin makaman a kasar.
Sanarwar hakan na zuwa ne mako guda kafin ganawar da Mr Kim zai yi da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in.
Kamfanin dillancin labaru na Koriya ta Arewa ya ambato Kim Jong-un na shaida wa kwamitin zartarwa na jam'iyyar Worker's Party wasu batutuwa shida inda daga ciki ya ce--babu wani muhimmanci a ci gaba da gwajin makaman nukiliya.
Koriya ta Arewa za ta sake harba makami mai linzami
Shugaban ya kuma ce zai maida hankali ne wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Hakan dai ya kara jaddada sakon sa ga 'yan kasar ne na sabuwar shekara inda a jawabin sa ya ce kasar ta gamsu cewa ita ma tana da karfin nukiliya.
Bayan gwajin makaman nukiliya har sau shida, Koriya ta Arewa na ganin bata bukatar kara fadada girmar nukiliyar ta.
Hakan dai ba yana nufin kawadda makaman nukiliyarta kwata-kwata bane kamar yadda kasashen duniya suka bukata, koda yake Koriya ta Arewa ta ce zata rufe tashoshinta na gwajin makaman, bata yi alkawarin ko zata yi watsi ba da makamanta.
A baya dai Pyongyang ta sha saba irin alkawuran da ta kan yi game da hakan.
Sai dai wannan wani muhimmin ci gaba ne da aka samu gabanin ganawar Kim Jong-un's shugaba Moon da kuma yiwuwar haduwar su da shugaban Amurka Donald Trump a karshen watan Mayu ko farkon watan Yuni.
Tuni Shugaba Donald Trump ya bayyana jindadin sa da wannan sanarwar.
Read More »

Thursday, 19 April 2018

LABARAI DA DUMI DUMINSA : An tsinci gawar yarinya 'yar shekara 3 da aka yi wa fyade a Kano

'Yan sanda a jihar Kano sun ce sun kama malaman wata makaranta su tara bayan da aka samu gawar wata yarinya da aka yi wa fyade.
An dai gano gawar yarinyar ne a cikin ajin makarantar kwanaki hudu bayan da iyayenta suka sanar da bacewarta.
An ce dai an gano gawar, wadda har ta fara rubewa kwance a cikin jini kuma tsirara.
Kakakin 'yan sandan jihar SP Magaji Musa Majiya, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce iyayen yarinyar wadda ba ta fi shekara biyu zuwa uku ba ne suka kai korafi ofishin 'yan sanda da ke unguwar Hotoro, suka ce 'yarsu da suka tura makarantar islamiyya ba ta dawo gida ba.
"An yi wa masu jego fyade"
Mata ta gantsara wa mai fyade cizo a mazakuta
''Yan daba sun sace' sandar majalisar dokokin Najeriya
Daga nan ne sai 'yan sandan suka fara neman yarinyar, kuma bayan kwana hudu sai aka gano gawar yarinyar a cikin wani aji da ke wata Islamiyya a Hotoron arewa a cikin wani yanayi.
SP Majiya, ya ce ya zuwa yanzu an tantance mutum uku daga cikin malaman makarantar ciki har da shugaban makarantar na bangaren boko da kuma malaman islamiyya biyu wadanda suke da makullin ajin da aka gano gawar yarinyar.
Kakakin 'yan sandan ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike a kansu har sai an gano wanda ya aikata wannan laifi ko kuma wanda ke da hannu akai.
Me ke jawo yi wa kananan yara fyade?
Matsalar fyade dai matsala ce da ta addabi al'ummar duniya baki daya, musamman fyaden da ake yi wa yara kanana wadanda ba suji ba su gani ba.
Likitoci dai sun ce wannan matsala na faruwa ne sakamakon ciwon ƙwaƙwalwar da ke damun mutanen da ke aikata fyaɗe.
Dr Attahiru Muhammad Bello, wani likitan ƙwaƙwalwa ne a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Adamawa, ya taba shaida wa BBC cewa matsalar gagaruma ce.
"Yawancin masu yi wa ƙananan yara fyade suna fama da cutar da a Turance ake kira paraphilia, wato jarabar bukatar yin jima'i, ko da kuwa da wani abu kamar ƙarfe ne ko kuma ƙananan yara."
Ya ce a kasashen da aka ci gaba ana sanya musu ido idan aka ga suna nuna irin wannan ɗabi'u tun suna yara ta yadda za a rika yi musu magani da ba su shawarwari.
'Tsattsauran hukunci'
Sai dai Malaman addini na ganin ana samun yawaitar fyaɗe musamman a kan kananan yara ne saboda neman abin duniya.
Dr Abdullahi Pakistan, wani Malamin addinin musulunci a birnin Kano ya ce abu uku ne ke haddasa wannan matsala:
"Tsananin neman duniya, inda za ka ga boka ko matsafi ya bukaci mutum ya aikata fyade ko ya cire agarar wani, ko kuma ya tono gawa domin biyan bukatunsa.
Sai kuma shaye-shaye da ke batar da hanakalin mutane ta yadda ba sa sanin abin da suke aikatawa, da kuma tasowa cikin rashin tarbiyya.
Mutane ba su san abin da ake kira tausayi ba. Duk mutumin da bai samu tausayi ba, ba zai tausayawa wani ba," a cewar babban malamin Islamar.
Malamin ya ƙara da cewa ya kamata hukumomi su rika yanke tsattsauran hukuncin kan duk mutumin da aka samu da laifin fyaɗe, sannan a gefe ɗaya kuma iyaye su duƙufa wajen yi wa 'ya'yansu tarbiyya baya ga wa'azi da Malamai za su mayar da hankali wajen yi wa al'umma kan illar wannan matsala.
Da alama dai wannan batu zai ci gaba da jan hankalin mutane a Najeriya, kuma zai ci gaba da kasancewa babban ƙalubale ga 'yan ƙasar da ma hukumomi, wadanda ake buƙatar su ɗauki matakai ƙwarara domin shawo kansa.
Read More »

Thursday, 30 November 2017

(video) Ban taba ambaton Sheikh Dahiru Bauchi a wa'azina ba — Kabiru Gombe

Babban sakataren kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Gombe, ya musanta cewa yana yawan ambaton sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi a cikin wa'azinsa.
Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai wa BBC a ofishinmu da ke Landan a makon daya gabata, inda ya ce shi a tarihin rayuwarsa bai taba ambaton sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba a cikin wa'azinsa.
Malamin addinin ya ce, "idan akwai wanda ke da wani kaset na wa'azinsa da ya ambaci sunan malamin, to kofa a bude take ya fiddo da shi ya yada wa duniya."
Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.
"Hasali ma shi shaihin shi ke ma ambatarmu a cikin wa'azinsa, domin ya kira sunana dana mahaifina ba sau daya ba, ya kuma kira shugaban kungiyarmu da sunansa karara, har ma ya kan siffantashi da munanan siffofi wanda shi shugaban bai taba mayar masa da martani a kan hakan ba," in ji shi.
Jagoran Izalan ya ce "ita da'awa ta ahlul sunnah ba da'awa ce ta kiran sunaye ba."
Read More »

Wednesday, 15 November 2017

An kashe wata yarinya a Nigeria don yin tsafi da sassan jikinta

'Yan sanda sun shaida wa BBC cewa an kashe wata yarinya 'yar shekara 17 a Najeriya don a sayar da sassan jikinta wajen yin tsafin da wasu suka yi amanna yana kawo arziki.
An kama mutum uku da suka hada da wani mutum wanda ya yi ikirarin kashe ta da sayar da sassan jikinta ga wani matsafi a kan dala 25, daidai da naira 9,000.
Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya kuma ce bayan haka ne kuma sai mutumin ya jefa gangar jikin yarinyar a wata rijiya da ke kauyen Idosemo a jihar Ogun. A Najeriya dai wasu mutanen sun yi amanna da al'amarin tsafi sosai.
A kan je wajen bokaye ko matsafa don neman maganin wasu cututtuka, kuma masu bin su sun yarda cewa suna da siddabarun da za su iya kawo musu sa'a a rayuwa.
Mai magana da yawun 'yan sandan Abimbola Opeyemi, ya ce matsafin, wanda tuni shi ma aka kama shi, ya bayyana cewa lallai ya karbi sassan jikin mutum, amma ya ce ba shi ya bayar da umarnin kisan ba.
Ya ce an kai wa yarinyar hari ne a lokacin da take talla a kan hanya. Mahaifinta ne ya kai rahoton batanta wajen 'yan sandan yankinsu. Mista Opeyemi ya ce, aikin hadin gwiwa da aka yi tsakanin 'yan sanda da 'yan sintiri ne ya sa aka kama matsafin, wanda ya amsa laifinsa a yayin da 'yan sanda ke tuhumarsa. Ya kara da cewa hakan ce ta sa har 'yan sanda suka gano rijiyar da aka jefa yarinyar. Har yanzu dai ba a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu ba.
Wannan kisan gilla dai shi ne na baya-baya da ya faru a kudu maso yammacin kasar, inda dama hakan na yawan faruwa.
Read More »

Tuesday, 14 November 2017

Dansanda ya yiwa soja dukan tsiya a wajen na’urar ATM dake Damaturu

Rundunar yansanda sun tafi da soja tare da dan sanda dan bincike al'amarin da ya janyo rikic ia tsakanin su Wani jami’in yansada ya ji ma wani soja rauni a lokacin da rikici ya barke a tsakinin su a wajen cire kudi a na'urar ATM dake Damaturu.
NAIJ.com ta samu rahoton cewa, rikicin ya fara na lokacin da wani soja ya zo cire kudi daga ATM, ya samu mutane suna bin layin cire kudi, amma shi yaki bi layin.
Mutanen da ke wajen suka nuna masa rashin amincewa akan zarar da yake so ya mu su, daganan wani dansanda dake cikin layin ya tunkari shi ya ce ma sa dole ya bi layi idan lallai yana son ya cire kudi daga na'urar ATM din.
Daganan rikci ya barke a tsakanin su, har suka fara kokuwa da juna, Dansanda ya samu galaba akan soja yayi masa dukan tsiya, har ya jima masa mumunar rauni a jiki. Rundunar yansadar 2ic dake Damaturu sun tafi da dansadar tare sojan dan bincike.
Daga Naijhausa
Read More »

Monday, 13 November 2017

Nigeria: An fara amfani da waka wajen yaki da cin hanci Ds Rashawa




A Najeriya, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, wato EFCC, ta rungumi wata sabuwar dabara ta amfani da mawakan Kannywood don shelar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin mata da yara.

Hukumar ta yi wani gangami a Kano, inda fitattun mawaka suka nuna basirarsu wajen isar da sakon hukumar ta hanyar waka. EFCC dai, ta bayyana cewa shigar da mata da yara a cikin yaki da cin hanci na da muhimmanci sakamakon matsayinsu a tsakanin al`uma kasancewar mata sune ginshikin tarbiyya ga yara da ake fatan su ne manyan gobe.
Dr Adamu Hamisu Danmusa, shi ne Daraktan ayyuka na hukumar EFCC mai kula da shiyyar arewa maso yamma ya ce, sun yanke shawarar fara amfani da mawaka ne domin isar da sakon da suke son isarwa ga al'umma musamman mata da yara a kan illar cin hanci.
Daraktan ya ce, mawaka ba bu inda ba sa isar da sako ta hanyar waka, don haka suke ganin amfani da mawakan zai taimaka wajen isar da sako ga al'umma, domin ba sai a rinka hada taruka don fadakar da mutane illar cin hanci ba.

Dr Adamu, ya ce dama an san mata da son waka, to ta hanyar waka za su isar da sakonni da dama.

A Najeriyar dai ana kukan cewa babu wani bangaren rayuwa da cin hanci bai ratsa ba. Najeriya dai kasa ce mai arzikin man fetur tun farashi na ganiyarsa, da wasu muhimman albarkatun kasa, ga kuma yawan jama`a, amma duk da haka galibin al`ummar kasar na fama da talauci sakamakon cin hanci da rashawa. Kodayake gwamnatin shugaba Buhari ta yi alwashin yaki da wannan annoba.
Read More »

Sunday, 12 November 2017

Yadda na hana zurarewar Naira biliyan 2.5 daga ma'aikata ta - Sheikh Isah Ali Pantami




Babban shehin malamin islamar nan, kwararre a harkokin sadarwar zamani kuma shugaban hukumar gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da ma'aitar ta National Information Technology Development Agency [NITDA] a turance, Sheikh Dakta Ali Isa Pantami ya bayyana kadan daga cikin cigaban da ya samu a ma'aikatar sa.

Shehin malamin dai ya bayyana cewa akalla makudan kudaden da suka kai darajar Naira biliyan biyu da rabi ne ya tattala, ya kuma hana su zurare tamkar a baya na gwamnatin tarayya a hukumar ta sa ta hanyar dabbaka wasu sabbin dubarun fasahohi.
NAIJ.com ta samu dai cewa shehin malamin ya bayyana hakan ne a cikin takardar bayan taro da suka fitar jim kadan bayan kammala tarin su na shekara-shekara mai taken e-Nigeria 2017 a garin Abuja, babban birnin tarayya.

Haka nan kuma Dakta Pantami ya kuma bayyana cewa kasar ta Najeriya tana bisa turbar da ya dace inda yace yanzu haka kasar na a sahun gaba sosai a nahiyar Afrika wajen samar da cigaban fasahar ta zamani.
Read More »

Sunayen wandanda ake zargin Karkatar Da Tirela 65 Na Abincin 'Yan Gudun Hijira

Sun Karkatar Da Tirela 65 Na Abincin 'Yan Gudun Hijira Wadanda Ake Zargin Masu Suna Adamu Ado Bomboy, Sadiq Abubakar Tijjani, Abba Thomas, Umar Idris Da Rabi'u Haruna, Yanzu Haka Ana Kan Tuhumarsu.
Daga Rariya Facebook
Read More »

Tuesday, 7 November 2017

EFCC ba ta bincike na – Sheikh Pantami

Shugaban Hukumar bunkasa fasahar sadarwar ta zamani ta Najeriya (NITDA), Sheikh Isa Pantami, ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake cewa Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa tana bincikensa. Wadansu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ruwaito Ministan Sadarwar kasar Adebayo Shittu yana cewa gwamnatin tarayya tana jiran sakamakon wani binciken da hukumar EFCC take wa shugabannin hukumar NITDA. Rahotannin sun ce ana binciken hukumar ne kan yadda ta kashe kudin da aka ware mata a kasafin kudin shekarar 2017, bayan wani korafi da aka gabatar a gaban hukumar EFCC. Sai dai Sheikh vPantami ya musanta hakan, "karya aka rubuta a kanmu kuma idan mun samu wadanda suka aikata hakan, to kotu za mu kaisu," in ji shi. Ya ce hukumar EFCC ba ta taba bincikarsa ba ko wani ma'aikacinsa tun da ya kama aiki da hukumar NITDA. "EFCC sanya mana albarka take game da kokarin da muke na kawo gyara a hukumar NITDA," kamar yadda ya ce. Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Pantami kan batun: BBC ta tuntubi mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, wanda ya ce: "ba zan iya cewa da gaske ne ana binciken hukumar NITDA ba, kuma ba zan iya cewa karya ba ne."
Read More »

Sunayen malaman da suka ci kashi 75 bisa 100 a jarabawar Kaduna

Sunayen wadanda suka ci kashi 75 bisa 100 a jarabawar gwaji da gwamnatin jihar Kaduna tayi wa malaman makarantun firamaren jihar. Shugaban hukumar SUBEB na jihar Nasir Umaru ya ce cikin malamai 33,000 da suka rubuta jarabawar 11,200 ne kawai suka sami nasarar cin kashi 75 bisa 100 na tambayoyin da aka yi musu. Ya Kara da cewa gwamnati ta Kafa wata kwamiti domin duba korafe-korafen da wasu malamai su keyi game da sakamakon jarabawar don bi musu hakkin su.
Read More »

Saturday, 28 October 2017

Ballagaza: Karuwanci Da Rayuwar Karuwai A Legas




Wani bincike ne mai zurfi ne na irin ayyukan yawancin karuwan da ke garin Legas gari ma fi yawan mutane a nahiyar Afirka, binciken ya kuma haɗa da kawalai da ke haɗa karuwan da mazaje a Unuguwannin Ɓictoria Island da Lekki da Ajah da sauran wuraren da ake gudanar harkoki na masha’a Kaman kulub-kulub in da sukan daɗu da hulɗarsu.
Karuwan kan samu gidaje a unguwanni masu tsada inda sukan kama haya su biyu ko uku a a ɗaki, kuma sun samu ƙwarewa ta musamman na yaudarar manyan masu kuɗi a wuri tatrurrukan aure kona “Birthday” da ire-iren su domin samun masu neman hulda da su.

LEADERSHIP A Yau ta gano cewa ɗaukar irin waɗannan matan na tsawon dare yana kamawa ne daga N30,000 zuwa N50,000 hakan ya kuma danganci wuri da waɗanda suka haɗa “Harkar” matan ne kan zaɓi wurin da za a yi “harkar” saboda dalilan tsaro in an cimma inda za a haɗu, matan kan zaɓi zuwa wurin “Haɗuwar ne a motar hawansu ko kuma a wasu motocin haya masu tsada wanda akasari suna da mambobin wayar direbobin, hakan, in ji Bella wata daga cikin waɗannan mata, yakan “ƙara maki daraja wajen abokin hurɗa yana kuma nuna cewa, kin fi ƙarfin ɗan ƙaramin kuɗi” “a kwai buƙatar kashe kuɗi waje kula da jikinki da gashinki kuma dole ki rinƙa sa kaya masu tsada in har kina son mazaje masu “tsada” su kula ki, ga kuma kuɗaɗen haya da sauran na harkokin yau da kullum shi ya sa kake gani matan na neman manyan kuɗaɗe in ba haka wata rana za a bar ki a baya” in ji ta. Bayan haɗu wa da “Kwastoma” ta hannun kawalai da kuma kai tsaye a wuraren haɗuwa na kulub-kulub, waɗannan matan sun kuma ƙware waje tallata kan su a hanyoyin sanarwa na zamani irin su Instagram da Snapchat da Facebook da Tinder da kuma irinsu Instachat sukan manna hotunansu tsirara tsirara domin yaudarar mazaje su nemi huɗa da su.

“ni ba na neman mazaje a kulub a Instagram nake haɗa harka na bayan mun daidaita da juna” in ji wata karuwar bayan da wakilinmu ya nemi ya yi huɗa da ita, ta bar shi tsaye, ta nufi wata babba mota ƙirar “Marsandi”, “amma fa ka sani ina da tsada domin na san hanyoyin gamsar da namiji” in ji ta. Jaridar LEADERSHIP A Yau ta kuma gano cewa, karuwai masu amfani da hanyoyin sadarwa na zamani kan chaji N50,000 zuwa N100,000 a dare ɗaya, ya wancin waɗannan matan kan yi amfani da waɗannan kuɗaɗe wajen kasuwanci a ƙasashen duniya irinsu Dubai, sukan kuma yi amfani da irin wannan tafiye tafiye samun wasu “ƙwastamomin masu romo” ta hanyar ayaudara mazaje da jikinsu da kuma kaya masu tsada das u ke sawa, hanƙoronsu a koda yaushe shi ne yadda za su tabbtar da akwai wani “ƙwastamomin masu romo” a komarsu. Amma a ɓangaren cikin garin Legas labarin daban ya ke a waje karuwan domin ko rabin takwarorinsu da ke harka a wurare irinsu ƁI da Ikoyi da Lekki da kuma Ajah a abin da ya shafi “Kwastoma” da kuma tsarin rayuwa da irin kuɗaɗen da su ke caza, haka kuma a kwai bambanci a irin wuraren da suke aikata masha’ar.

Misali a wurare irin su Ikeja da Maryland da Yaba da Surulere da Ojodu da kuma Ogudu wuraren da matsayin rayuwa ke matsakaici kuɗaɗen da karuwai kan caja ya yi ƙasa sosai akan abin da takwarorinsu na Ɓictoria Island, kasancewa da karuwa a waɗannan unguwanni da tsawon dare kan buƙaci N5,000 zuwa N10,000 hakan ma ya danganta ne da wuri da kuma yanayin da aka haɗu. Yawancin waɗannan matan zaka samu ba su da motoci da gidaje na kansu da za su kai “kwatamominsu” sukan dogara ne a kan shi “mutumin ya ɗauke su zuwa inda za su yi harkar, su kuma masu neman na “sha yanzu magani yanzu” ya kan kama daga N1,500 zuwa N2,500. “Da yawa a cikinmu ke ɗaukar ɗawainiyar gidajenmu, saboda haka ne mu kan hurɗa da mutum dai dai gwargwadon aljihunsa” in ji Joy, wadda ke harkar karuwancinta a unguwannin Yaba da Mushin a yayin da take zantawa da wakilinmu. “ a kwai lokuttan da babu kwastoma, to dole ki yarda da mutum ko da nawa ya maki da shi, wasu lokuttan kuma in kasuwa ta buɗe har N7,000 mu kan karɓa a kwanan gida” in ji ta.

Joy, kamar yawancin mata a nan ɓangaren sun shafe fiye da shekara 5 suna karuwanci amma babu wani abin a zo a gani da suka ƙulla, ba kamar takwarorinsu na na yankin Ɓictoria Island ba wayenda suke gudanar da babbar harka, kuma basu fuskantar wata tsangwamar ‘yansanda da ‘yan iska kamar yadda ake yawan kai samame a waccan ɓangaren.
“In ba ki yi saa ba ‘yan sanda ko ‘yan iska sukan kwace ɗan abin da ki ka samu, yawancinmu mun fi shekara 5 muna karuwanci amma babu wani abin kirki da muka tara, ba don muna ɗan samun na cin abinci ba da ɗan abin da muke tura wa wa iyayenmu da ire-irena mun bar wannan sana’ar” yarinyar ta ƙara bayyanawa.

Banda rayuwa a kan titi da sauran bambance-bambance da ke tsakanin karuwan Ɓictoria Island dana cikin garin Legas, su na unguwanni kamar Lekki da Ikoyi da Ajah kan haɗu da mazaje ne ta hanyoyin sadarwa na zamani amma a kan kuma biya su kuɗaɗen harkarsu ne ta hanyar biya kai tsaye zuwa asusun ajiyarsu ta bankinsu, su kosu ko
na cikin gari sukan bayyanar da tsiraicinsu ne Kai tsaye a wuraren shan barasa da ka tituna in da yawancin mazajen da ke halartar wuraren na neman mata ne masu arha kuma yawancin na wuraren ne ‘yan iska da ɓarayi ke shawagi abin da kan sa karuwan kan rasa kayayyakinsu kamar wayar salula a wasu lokutta ma ‘yan iskan kan lakaɗa masu kasha bayan yin lalata da su, irin waɗannan matan kan faɗa hannun miyagu matsafa, bayani ya nuna cewa karuwai da yawa ne suka mutu ta wannan hanyar. Jima’I da wani abun ne da Allah Ya halasta ma ma’aurata, amma yanzu ya zama wani abin da zaka gani a lowanne lungu na ƙasar nan, mata na tallarsa maza na saya, an ƙiyasta cewa miliyoyin nairori a ke samu a harkar karuwanci a duk faɗin ƙasar a kowanne shekara, wannan bunƙasar ne ya haɓɓaka ƙaruwar gidaje otal-otal da gidajen masha’a a Legas da manyan garuruwa a lungunar ƙasar nan, duk da cewa karuwanci haram a dokokin ƙasar nan amma harkar na matuƙan bunƙasa saboda tsnanin rashin aikin yi da ake fama da shi da “alherin” da ke fitowa daga wannan mummunan sana’a.
Read More »

KADAN YA RAGE A DAMBACE TSAKANIN ABIDA MOH'D DA RASHEEDA MAI SA'A

DUK da cewar taron kungiyar mata masu aure ’yan fim da aka yi a Kano kwanan nan an yi shi an gama lafiya, sai dai kadan ya rage a dambace tsakanin Abida Mohammed da Rasheeda Adamu Abdullahi. A gaskiya, ba don shiga tsakani da aka yi ba, aka shawon kan su, to da kyar da tuni labari ya canza. Lamarin dai ya auku ne bayan an tashi daga taron. A daidai lokacin da mutane su ke fitowa daga wajen, sai kawai aka ji hayaniya ta kaure tsakanin jaruman biyu, wadanda a can baya aminan juna ne da ko barci ba ya raba su. Babu dai wata cikakkiyar magana a game da abin da ya hada su fada a wajen, amma dai a lokacin da Rasheeda ta ke fitowa daga dakin taron an ji ta ta na fada tare da yarfar da habaici ba tare da an san ko da wa ta ke ba. Amma fitowar Abida da kuma yadda su ka shiga fada wa juna bakaken maganganu shi ne ya sa aka fahimci inda maganar Rasheeda ta dosa. Sun shafe tsawon kusan minti 30 su na ta cacar baki da gori da tonon silili a tsakanin su, har ma da kokarin kai wa juna duka. Abida ce ta fi zakewa a wajen kai dukan, ana ta rirrike ta, yayin da ita kuma Rasheeda aka yi kokarin saka ta a motar ta. Hakan bai sa Abida ta janye kudirin ta na kai wa Rasheeda duka ba. Jama'a sun cika wajen, ciki har da masu wucewa, su ka tsaya su na kallo. Abin dai babu tsari, sai wanda ya gani! An samu shawo kan fadan ne a lokacin da Saima Mohammed ta fito daga dakin taron, ta ga abin da ya ke faruwa, don haka ta je ta shiga tsakin su. Ganin girman ta ne ya sa Rasheeda ta ja motar ta, ta bar wajen, yayin da ita kuma Abida aka janye ta da karfin tsiya.
Read More »
Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie