Pages

Games

Wednesday 25 April 2018

Labaran duniya : An gano zuciyar Sarauniyar Faransa da aka sace

'Yan sandan a Faransa sun gano wani akwatin zinari da ke dauke da zuciyar daya daga cikin wata jaruma, wadda aka sace daga wani gidan adana kayan tarihi a makon jiya.
Akwatin wanda yake dauke da kayayyaki mallakin Sarauniya Anne, an kera shi ne a karni na 16.
'Yan sanda sun kama mutanen biyu a ranar Asabar kuma sun kai su inda aka binne akwatin kusa da birnin San Nazaire da ke yammacin kasar.
Anne kadai ce macen da aka taba nada wa Sarauniyar Faransa sau biyu.
An ce tana daya daga cikin mata mafiya arziki, kuma aka fara yi wa alkawarin auren Yarima Edward na Ingila.
Me ya sa Atiku ke son shugabancin Najeriya?
'An tsinci yara 26,000 a titunan jihar Kano'
Yadda 'yan Afirka suke fama da wariyar launin fata
Amma yariman ya yi batan-dabo lokacin yana yaro, tare da dan uwansa Richard - an zargin kawunsa King Richard III da sanadiyyar bacewarsu.
Daga baya Anne ta auri 'yan gidan sarautar Faransa guda biyu, Charles VIII a 1491 sannan kuma dan uwansa Louis XII a shekarar 1498.
Akwatin zinarin yana da nauyin Gram 500 da siffar zuciya, yana kuma da rubutun tsohon harshen Faransanci a jikinsa.
Hukumomin kasar sun bukaci a dawo da akwatin, don sun yi imani da cewa barayi ba su fahimci muhimmancin tarihin zuciyar ba, wanda aka kubuta daga narkewa bayan juyin juya halin Faransa a shekarar 1789.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie