A Najeriya, wasu mukarraban shugaban kasar sun ce an yi mummunar fahimta game da kalaman da shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa mafi yawan matasan kasar ci-ma zaune ne.
Shugaba Buhari yana magana ne a taron kasashen renon Ingila dake gudana a birnin Landan.
Sai dai kalaman sa na ci gaba da tayar da kura a tsakanin matasan kasar musamman a kafafen sada zumunta na zamani.
Matasa da dama dai sun nuna damuwarsu kan kalaman da suka ce na zubar da kima ne.
'Yan Nigeria na da gajen hakuri — Buhari
Abin da ya sa na yi wa Buhari uzuri - Soyinka
Sai dai mai bai wa shugaban shawara kan kafafen watsa labarai Sha'aban Sharada, ya ce matasa ba su fahimci kalaman Shugaba Buhari ba.
Ya ce "duk wanda ya kalli bidiyon Shugaba Muhammadu Buhari zai ga cewa ya furta kalaman ne cikin raha".
Sha'aban Sharada wanda ke cikin 'yan tawagar shugaban kasar da ke ziyara a Landan ya ce furucin da Shugaba Buhari ya yi hannunka mai sanda ne ga al'ummar kasar domin su tashi tsaye wajen neman na kansu.
Ya ce a ko wanne lokaci batun yadda za a inganta rayuwar matasa shi ne babban abun da Shugaba Buhari ya sa a gaba.
Ce-ce-ku-ce
Matasa a Najeriya sun yi ta ce-ce-ku-ce tare da mayar da martani kan kalaman Shugaba Buharin, musamman a shafuka sada zumunta.
Wasunsu sun yi ta yi wa shugaban ba'ar cewa ai matasan ne suka yi tsaiwar-daka har ya zama shugaban kasa.
To sai dai duk da haka akwai wasu matasan da suke ganin babu aibu a maganar shugaban, domin kuwa bai hada matasan ya yi musu kudin goro ba, ya dai ce da dama daga cikinsu ne suka da wannan matsala.
Haka kuma wasu na da ra'ayin cewa gaskiya ce zalla shugaban ya fada, don haka babu wani abin tada jijiyar wuya.
No comments
Post a Comment