Tsohuwar fitacciyar jarumar shirin fina finan Kannywood, Rukayya Dawayya ta bayyana matsalolin data fuskanta a rayuwar aure da suka yi sanadin mutuwar auren nata da tsohon mijinta.
Dawayya ta bayyana haka ne a wata hira da tayi da jaridar Blue Print, inda tace tayi danasanin auren tsohon mijinta Adamu Teku, saboda bata yi cikakken bincike ba game da shi. Auren Dawayya ya mutu ne kimanin shekaru hudu bayan auren, a lokacin da ta kai ma mahaifiyarta ziyara bayan dawowarta Najeriya daga kasar Saudiyya, duk kuwa da sadaukarwar da ta dinga yi don ganin auren ya zauna lafiya.
“Allah na gani na yi iya bakin kokarina don ganin aurena ya zauna lafiya, amma hakan bai yiwu ba, saboda mijina auri saki ne, kafin ni ma ya saki mata sama da 15, don haka ba kai na farau ba. Yarona Arafat ne na 11 a cikin yayansa.
“Banda matan da ya saka kafin su haihu a gidansa, Uwargidarsa ta bayyana min cewar kafin ita ma ya auri mata guda 6, itace ta 7 a yanzu. Kuma gaskiya ban yi bincike game da shi ba a sosao kafin aurenmu, iyakar binciken da nayi shine a Abuja, amm banke kauyensu ba a jihar Adamawa.
“Don har babbar yarsa sai da bayyana min dukkanin halayyarsa, har ma a kauyensu ana cin mutuncin yayansa da sunan wai mahaifinsu baya iya rike matan aure, wanda hakan ya sanya yayan nasa basa iya cudanya da jama’an kauyen.” Inji ta.
Bugu da kari da aka tambayeta game tsawon lokacin da suka yi suna soyayya kafin aure, sai Dawayya tace gaskiya watanni biyu suka yi kacal suna soyayya, sakamakon a wannan lokacin aure kawai take son yi ruwa a jallo, don haka ta rungumeshi ba tare da bata lokaci ba, har suka yi aure.
Daga karshe Dawayya tace tun bayan da ta samu juna biyu ne Adamu ya fara nuna mata fushinsa, saboda wai shi baya son haihuwa, don haka ya gindaya mata munanan sharudda, amma ta cije, har sai ranar da ta kai ma mahaifiyarta ziyara, inda ya aiko mata da sakon saki ta wayar hannu
No comments
Post a Comment