'Yan sanda a jihar Kano sun ce sun kama malaman wata makaranta su tara bayan da aka samu gawar wata yarinya da aka yi wa fyade.
An dai gano gawar yarinyar ne a cikin ajin makarantar kwanaki hudu bayan da iyayenta suka sanar da bacewarta.
An ce dai an gano gawar, wadda har ta fara rubewa kwance a cikin jini kuma tsirara.
Kakakin 'yan sandan jihar SP Magaji Musa Majiya, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce iyayen yarinyar wadda ba ta fi shekara biyu zuwa uku ba ne suka kai korafi ofishin 'yan sanda da ke unguwar Hotoro, suka ce 'yarsu da suka tura makarantar islamiyya ba ta dawo gida ba.
"An yi wa masu jego fyade"
Mata ta gantsara wa mai fyade cizo a mazakuta
''Yan daba sun sace' sandar majalisar dokokin Najeriya
Daga nan ne sai 'yan sandan suka fara neman yarinyar, kuma bayan kwana hudu sai aka gano gawar yarinyar a cikin wani aji da ke wata Islamiyya a Hotoron arewa a cikin wani yanayi.
SP Majiya, ya ce ya zuwa yanzu an tantance mutum uku daga cikin malaman makarantar ciki har da shugaban makarantar na bangaren boko da kuma malaman islamiyya biyu wadanda suke da makullin ajin da aka gano gawar yarinyar.
Kakakin 'yan sandan ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike a kansu har sai an gano wanda ya aikata wannan laifi ko kuma wanda ke da hannu akai.
Me ke jawo yi wa kananan yara fyade?
Matsalar fyade dai matsala ce da ta addabi al'ummar duniya baki daya, musamman fyaden da ake yi wa yara kanana wadanda ba suji ba su gani ba.
Likitoci dai sun ce wannan matsala na faruwa ne sakamakon ciwon ƙwaƙwalwar da ke damun mutanen da ke aikata fyaɗe.
Dr Attahiru Muhammad Bello, wani likitan ƙwaƙwalwa ne a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Adamawa, ya taba shaida wa BBC cewa matsalar gagaruma ce.
"Yawancin masu yi wa ƙananan yara fyade suna fama da cutar da a Turance ake kira paraphilia, wato jarabar bukatar yin jima'i, ko da kuwa da wani abu kamar ƙarfe ne ko kuma ƙananan yara."
Ya ce a kasashen da aka ci gaba ana sanya musu ido idan aka ga suna nuna irin wannan ɗabi'u tun suna yara ta yadda za a rika yi musu magani da ba su shawarwari.
'Tsattsauran hukunci'
Sai dai Malaman addini na ganin ana samun yawaitar fyaɗe musamman a kan kananan yara ne saboda neman abin duniya.
Dr Abdullahi Pakistan, wani Malamin addinin musulunci a birnin Kano ya ce abu uku ne ke haddasa wannan matsala:
"Tsananin neman duniya, inda za ka ga boka ko matsafi ya bukaci mutum ya aikata fyade ko ya cire agarar wani, ko kuma ya tono gawa domin biyan bukatunsa.
Sai kuma shaye-shaye da ke batar da hanakalin mutane ta yadda ba sa sanin abin da suke aikatawa, da kuma tasowa cikin rashin tarbiyya.
Mutane ba su san abin da ake kira tausayi ba. Duk mutumin da bai samu tausayi ba, ba zai tausayawa wani ba," a cewar babban malamin Islamar.
Malamin ya ƙara da cewa ya kamata hukumomi su rika yanke tsattsauran hukuncin kan duk mutumin da aka samu da laifin fyaɗe, sannan a gefe ɗaya kuma iyaye su duƙufa wajen yi wa 'ya'yansu tarbiyya baya ga wa'azi da Malamai za su mayar da hankali wajen yi wa al'umma kan illar wannan matsala.
Da alama dai wannan batu zai ci gaba da jan hankalin mutane a Najeriya, kuma zai ci gaba da kasancewa babban ƙalubale ga 'yan ƙasar da ma hukumomi, wadanda ake buƙatar su ɗauki matakai ƙwarara domin shawo kansa.
No comments
Post a Comment