Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa dan majalisar dattijan kasar mai wakiltar jihar Kogi ta Arewa, Dino Melaye yana hannunta.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriya, Aremu Adeniran ya tabbatar wa BBC cewa Sanata Melaye yana hannunsu.
Ya kuma ce shi ne ya mika kansa a safiyar Talata, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter gabanin yin hakan.
Aremu Adeniran ya ce za su ci gaba da tsare Sanata Melaye har sai bayan sun kammala binciken da suke yi a kan zargin da ake yi masa.
A ranar Litinin ne dai 'yan sanda suka yi dirar mikiya a gidan dan majalisar a unguwar Maitama da ke Abuja bayan da jam'ian hukumar shige da fice suka kama shi yayin da yke shirin fita daga Najeriya.
Amma daga bisani an sako shi.
A kwanakin bayan ne rundunar 'yan sandan kasar ta bayyana dan majalisar dattawan a matsayin wanda suke nema ruwa-a-jallo.
'Yan sandan na zarginsa da kin bayyana a gaban kotu domin fuskantar shari'a kan zargin daukar nauyin wasu mutane su tayar da hankali da aikata miyagun laifuka.
Sai dai sanatan ya yi watsi da dukkan zarge-zargen yana mai cewa siyasa ce kawai.
An bai wa 'yan sandan duniya umarnin kama Dino Melaye
'Yan sandan Najeriya makaryata ne - Dino Melaye
Sanata Dino Melaye, wanda na hannun damar Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne, yana jawo ke-ce-kuce saboda kalamansa na siyasa da kuma salonsa na son rayuwar kasaita.
Dino Melaye a takaice
Dan asalin jihar Kogi, amma an haife shi a Kano
Shekararsa 44
Ya yi karatun firamare a Kano
Ya yi digirinsa a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria
Yana wakiltar Kogi Ta Yamma a majalisar dattawa
Ya taba zama dan majalisar waklilan Najeriya har sau biyu
An san shi a tarar aradu da ka a harkokin siyasa
Ya taba karbar lamar yabo na dan majalisar wakilan da babu kamarsa daga wata kungiyar matasa
Karin labaran da za ku so ku karanta:
Dino Melaye ya fito a wakar hip-hop
Nigeria: An yi hatsaniya yayin zanga-zangar Dino Melaye
No comments
Post a Comment