Assalam Sako Na Musamman Da Fitaccen Mawakin Fina Finan Hausa Nara M Inuwa
Game Da Sababbin Album's Ɗinsa Masu Zuwa A Shekara Mai Zuwa Masu Suna MAI ZAMANI Album da ANGO Album
Hausawa Dai Dama Sunce Ita Waƙa A Bakin Mai Shi Tafi Daɗi Gadai Sanarwar Daga Nura M Inuwa Kai Tsaye
NURA M INUWA
Assalamu alaikum warahmatulla hi ta'ala wabara katuhu, bayan sallama irin ta addinin musulunci,
ina yiwa ƴan uwa da masoya fatan alkhairi, kamar yadda aka saba barkan mu da shigo wa sabuwar shekara, alkhairan dake cikin ta Allah ya haɗa mu dashi, ya kuma tsare mu da dukkanin sharruka
Da wannan zanyi amfani wajan tallata muku sabbin Album's ɗina, wanda na sawa suna Mai Zamani, sabon Album ɗin Mai Zamani, yana ɗauke da darussa wanda bazan iya cewa komai a kansu ba
Kama daga kan faɗakarwa, nishaɗan tarwa, da kuma Soyayya, sai dai kun ji shi
fata na karku gajiya wajan jinkirin kawo muku sabbin Album's ɗina a kai a kai da banayi,
Sai na biyu kuma wanda na bashi suna ANGO Album, zanso kuji abinda yake ɗauke a cikin sa zasu zo muku ne a tare insha Allahu
Karda ku manta sunan su ANGO da Mai Zamani, tunani na gansuwar Ku, farin ciki na nishaɗin ku, ni ne naku-naku har kullum Nura M Inuwa
Impomation
ReplyDeleteIna wakokin
ReplyDelete