Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood watau Rahama Sadau, ta bayyana a ranar Asabar din da ta gabata cewar, ta soma shiga matsalolin rayuwa ne tun bayan da ta fara fitowa a shire-shiren fina-finan kudancin kasar nan ta Najeriya da aka fi sani da Nollywood.
Jarumar dai wadda aka dakatar da ita daga fina-finan Hausa a shekarar 2016 ta bayyana yadda tace ta na shan bakar ukuba daga ‘yan uwan sana’ar ta na watau jaruman masana’antar Kannywood.
Jarumar ta kuma ce tabbas ba abu ne mai dadi ba kwata-kwata yadda ta ke shan tsangwama a wasu lokuttan idan mutun ya tsallaka zuwa shirin finafinai na kudanci ko na turawa musamman ma don dai yadda al’adu da dabi’u suka banbanta kawai.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa har yanzu dai jarumar na cikin dambarwa da jiran tsammani tun bayan dawowar ta daga kasar Turkiyya inda ta shafe akalla watanni uku tana wani karatu yanzu kuma ta dawo gida tana jiran kungiyar su ta masu shirya fina-finan watau MOPPAN ta dake dakatarwar da ta yi mata.
No comments
Post a Comment