Pages

Games

Monday 23 April 2018

Labaran wasanni : Barcelona ta dauki Copa del Rey bayan lallasa Sevilla 5-0

Barcelona ta dauki kofin Copa del Rey karo na hudu a jere bayan da ta lallasa Sevilla da ci 5-0, ranar Asabar, a filin Atletico Madrid, Wanda Metropolitano.
Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci Barcelona ta ci 3-0, inda Luis Suarez ya fara daga raga a minti na 14, bayan da Philippe Coutinho ya saka masa kwallon.
Lionel Messi ne ya zura ta biyu, kuma bal dinsa ta 40 da ya ci wa kungiyar a bana a minti na 31 da fara wasa.
Suarez ya kara ta uku bayan da Messi ya saita masa bal din ana saura minti biyar a tafi hutun rabin lokaci.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 52 Andres Iniesta ya ci bal ta hudu, kafin kuma Philippe Coutinho ya ci ta biyar da bugun fanareti, wand hakan ya sa Barcelona daukar kofinta na farko tun lokacin da kociynta Ernesto Valverde ya kama aiki a watan Mayu.
Sevilla wadda ta doke Atletico Madrid ta samu gurbin wasan na dab da na karshe ba ta yi wani katabus ba a wasan da Barcelona ta mamaye a filin Atletico na Wanda Metropolitano.
Barcelona za ta iya daukar kofi na biyu inda za ta daga na La Liga a ranar Lahadi, idan ta biyu a tebur Atletico Madrid ta sha kashi a hannun Real Betis, a karawar da za su yi da karfe 7:45 na dare agogon Najeriya.
A haduwa tara da suka yi a karshen nan Sevilla ba ta taba doke Barcelona ba, kuma rabonta da cin wasa tun bayan da ta fitar da Manchester United daga gasar kofin zakarun Turai, ranar 13 ga watan Maris.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie