Pages

Games

Saturday, 21 April 2018

Labaran duniya : Koriya ta Arewa ta dakatar da shirinta na nukiliya

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya sanar da cewa ba zai sake gwajin harba makamai masu linzami ba, kuma zai rufe tashoshin da ake gwajin makaman a kasar.
Sanarwar hakan na zuwa ne mako guda kafin ganawar da Mr Kim zai yi da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in.
Kamfanin dillancin labaru na Koriya ta Arewa ya ambato Kim Jong-un na shaida wa kwamitin zartarwa na jam'iyyar Worker's Party wasu batutuwa shida inda daga ciki ya ce--babu wani muhimmanci a ci gaba da gwajin makaman nukiliya.
Koriya ta Arewa za ta sake harba makami mai linzami
Shugaban ya kuma ce zai maida hankali ne wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Hakan dai ya kara jaddada sakon sa ga 'yan kasar ne na sabuwar shekara inda a jawabin sa ya ce kasar ta gamsu cewa ita ma tana da karfin nukiliya.
Bayan gwajin makaman nukiliya har sau shida, Koriya ta Arewa na ganin bata bukatar kara fadada girmar nukiliyar ta.
Hakan dai ba yana nufin kawadda makaman nukiliyarta kwata-kwata bane kamar yadda kasashen duniya suka bukata, koda yake Koriya ta Arewa ta ce zata rufe tashoshinta na gwajin makaman, bata yi alkawarin ko zata yi watsi ba da makamanta.
A baya dai Pyongyang ta sha saba irin alkawuran da ta kan yi game da hakan.
Sai dai wannan wani muhimmin ci gaba ne da aka samu gabanin ganawar Kim Jong-un's shugaba Moon da kuma yiwuwar haduwar su da shugaban Amurka Donald Trump a karshen watan Mayu ko farkon watan Yuni.
Tuni Shugaba Donald Trump ya bayyana jindadin sa da wannan sanarwar.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie