Pages

Games

Thursday 26 April 2018

Siyasa Nigeria : Dalilan da suka sa muka gayyaci Buhari - Yakubu Dogara

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya ya yi karin haske kan dalilan da suka sa majalisar ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a gabanta domin ya yi bayani kan yawan kashe-kashen jama'ar da ake yi a fadin kasar.
Yakubu Dogara ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa hakkin gwamnati ne ta samar da tsaro ga al'ummarta, a don haka majalisar "ba za ta zuba ido tana gani ana kashe jama'a ba".
Matakin da majalisar ta dauka ya biyo bayan bukatar da dan majalisa Mark Gbilah daga jihar Benue, inda aka kashe mutum 16 ciki har da limaman coci biyu ranar Litinin, ya gabatar mata ne.
Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankula a bana tsakanin manoma da makiyaya a sassan kasar da dama.
Rikicin na Benue da ma wasu sassan kasar, na kara matsa lamba kan Shugaba Buhari a daidai lokacin da zabe ke kara karatowa.
Kudurin da aka gabatar a majalisar ya nemi Shugaba Buhari ya bayyana domin tattauna wa kan kashe-kashen na Benue da ma sauran yankunan kasar.
Kawo yanzu ba a bayyana lokaci ko ranar da shugaban zai bayyana ba, kuma babu wani martani ya zuwa yanzu daga fadar gwamnatin kasar kan wannan sammaci.
Gaddafi ne ya bai wa makiyaya makamai - Buhari
Abin da ya sa na nemi
Hon Yakubu Dogara ya kara da cewa "Dangane da karuwar hare-hare kan jama'ar gari a sassan kasar nan, mun kada kuri'ar yanke kauna kan hafsoshin sojin kasar nan kuma mun nemi a ciresu daga mukamansu".
"Babban hakkin gwamnati shi ne ta tsare rayuka da dukiyar al'ummarta, a don haka a matsayinmu na 'yan majalisar da suka san abin da ya kamata, ba za mu ci gaba da zuba ido muna kallo ana kashe jama'a ba".
Wasu 'yan kasar da dama dai na nuna rashin gamsuwarsu kan yadda gwamnatin ke tunkarar batun rikice-rikicen.
Sai dai gwamnatin ta Shugaba Buhari, wanda aka zaba saboda alkawarin samar da tsaro, ta nace cewa tana daukar matakan da su ka dace domin shawo kan lamarin.
Rikicin manoma da makiyaya
Rikicin manoma da makiyaya dai a Najeriya ya yi sanadin asarar rayuka daga dukkan bangarorin biyu, al'amarin da ya jawo hankalin kusan daukacin 'yan Najeriya.
Rikicin ya fi kamari ne a jihohin Filato da Benue da Taraba da Nassarawa da Kaduna.
A baya gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa su samar da wuraren kiwo.
Sai dai gwamnonin sun yi fatali da wannan kira, suna masu cewa ba su da isassun filayen da za su bayar domin kiwo.
Amma a watan Fabrairu Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gayyaci Fulani makiyaya su koma jiharsa domin gudanar da kiyo ba tare da samun matsala ba.
Bayani kan ShugabaBuhari a takaice:
Shekararsa 75
An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
An hambare shi a juyin mulki
Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
Musulmi ne daga arewacin Najeriya
Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie