Wata babbar motar daukar yashi ta yi mummunan hadari a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya inda ta abka ta doki fililon babbar gada a unguwar Mabushi.
Hadarin ya faru ne da yammacin Laraba a daidai lokacin da ake tashi daga aiki.
Hadarin ya shafi wasu motocin tasi guda biyu inda akalla mutane 5 suka mutu.
Rahotanni sun ce rashin birki ne ya sa babbar motar da doki ginshikan babbar gadar.
Da farko motocin tasi guda biyu ne suka fara yin hadari a kasan gadar da ke zuwa Gwarinpa.
Bayan isowar jami'an tsaro suna kokarin diba hadarin 'yan tasi, sai ga babbar motar a guje kuma a lokacin da suke kokarin tsayar da shi, rahotanni suka ce ya abka ginshikan gadar.
Wasu shaidu sun ce direban babbar motar ya yi ta yi wa jami'an tsaro hannu su kauce saboda ba ya da birki, kafin ya ci birki da ginshikan babbar gadar a Abuja.
Mutanen da ke cikin babbar motar dai babu wanda ya fita, dukkaninsu sun mutu
An shafe lokaci ana kokarin fitar da gawar yaron babbar motar da direba wadanda kan motar ya game da su a ginshikan gadar
Wannan dai wani mummunan al'amari ne da ya faru a Abuja wanda ya haifar da cunkuson mutane da ababen hawa.
No comments
Post a Comment