Gwamnatin Birtaniya ta bukaci babbar likitar gwamnatin kasar da ke aikin tiyatar gaban mace da ta bayar da sabuwar kididdiga a kan yawan matan da aka yi wa tiyata a gabansu.
Tun a shekarar 2008, aka yi wa mata dubu 27,016 irin wannan aiki na sanya musu wata raga a gabansu idan suna fama da matsalar kasa rike fitsari ko kuma idan gabansu ya dan saki domin ta taimaka musu.
To amma, kididdiga ta nuna cewa an cire wa mata 211 ragar.
Matan dai suna korafin cewa ragar da aka sanya musun tana janyo musu matsala a gaban nasu, shi ya sa suke zuwa a cire.
Yanzu dai gwamnatin Birtaniya ta bukaci da a ba ta sabuwar kididdiga a kan adadin matan da aka yi wa wannan tiyata a cikin wata guda.
Me zai sa miji ya yi wa matarsa komai a duniya?
Ana zargin R Kelly da sanya wa wata mata ciwon sanyi
Matsayin musulunci kan sanya turare a al'aurar mace
Wata sabuwar kididdiga da hukumar inshorar lafiya ta Birtaniya ta fitar, ta nuna cewa an yi wa mata 21 tiyatar cire ragar da aka sanya musu a tsakanin shekarun 2016-17, ragi a kan wadanda aka cire wa a shekarar 2015, kuma ya haura zuwa 40 a shekarun 2011-12.
A shekarar 2016-17 mata 2,680 a ka yi wa tiyatar idan aka kwatanta da mata 3,413 da a ka yi wa aiki a shekarar 2011-2012.
Ministan lafiya na kasar, Lord O'Shaughnessy, ya ce ana bukatar kididdigar ne saboda a gano adadin matan da ake yi wa irin wannan tiyata a kasar.
Ya ce, saboda muhimmancin al'amarin, aka bai wa shugabar likitocin da ke irin wannan tiyata Farfesa Dame Sally Davies, damar ta ji ra'ayoyin ma'aikatan hukumar inshorar lafiyar da kungiyar likitoci masu tiyata, da kuma kungiyar matan da aka yi wa irin tiyatar da suka samu matsala bayan aikin.
Karin bayani
An dai kiyasta cewa, an yi wa mata dubu 100 tiyata a gabansu ta hanyar sanya musu wata raga da za ta tallafawa gaban nasu a Ingila.
Mafi yawancinsu dai ba su samu wata matsala ba bayan tiyatar.
Kazalika wasu mata fiye da 800 sun dauki matakin shari'a a kan hukumar inshorar lafiya ta kasar bayan an yi musu tiyatar.
Ba kasafai ake irin wannan tiyata a wasu kasashen duniya ba, musamman kasashen Afirka, domin da yawa mutane ma ba su san ana irin tiyata ta sanya raga a gaban mace idan gaban nata ya samu matsala ba.
Me zai sa budurwa shan kayan mata?
Adikon Zamani: Illar tallace-tallacen 'yan mata
No comments
Post a Comment