Akalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu, bayan wani hari da aka kai wata cocin darikar katolika watau St Ignatius Catholic Church a jihar Benue kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.
Wadansu mahara ne wadanda gwamnatin jihar ta ce makiyaya ne suka kaddamar da harin a garin Ayar-Mbalom da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas.
Kuma cikin mutanen da aka kashe har da limaman coci guda biyu.
Har ila yau maharan sun kona akalla gidaje kimanin 50, a cewar gwamnatin jihar ta bakin mai magana na yawun jihar Terver Akase.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan, gami da mika jaje ga gwamnati da al'ummar jihar.
Ya ce kisan mutanen a coci "aikin shaidanci ne,kuma yunkuri ne na haddasa rikicin addini, da janyo mummunan zubar da jini."
Wata sanarwa da kakakin gwamnatin Femi Adesina ya fitar ta ce, Shugaba Buhari ya sha alwashin zakulo maharan da kuma hukunta su.
Jihar Benue jihar ta dade tana fama da rikicin makiyaya da manoma.
No comments
Post a Comment