Pages

Games

Sunday, 12 November 2017

Yadda na hana zurarewar Naira biliyan 2.5 daga ma'aikata ta - Sheikh Isah Ali Pantami




Babban shehin malamin islamar nan, kwararre a harkokin sadarwar zamani kuma shugaban hukumar gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da ma'aitar ta National Information Technology Development Agency [NITDA] a turance, Sheikh Dakta Ali Isa Pantami ya bayyana kadan daga cikin cigaban da ya samu a ma'aikatar sa.

Shehin malamin dai ya bayyana cewa akalla makudan kudaden da suka kai darajar Naira biliyan biyu da rabi ne ya tattala, ya kuma hana su zurare tamkar a baya na gwamnatin tarayya a hukumar ta sa ta hanyar dabbaka wasu sabbin dubarun fasahohi.
NAIJ.com ta samu dai cewa shehin malamin ya bayyana hakan ne a cikin takardar bayan taro da suka fitar jim kadan bayan kammala tarin su na shekara-shekara mai taken e-Nigeria 2017 a garin Abuja, babban birnin tarayya.

Haka nan kuma Dakta Pantami ya kuma bayyana cewa kasar ta Najeriya tana bisa turbar da ya dace inda yace yanzu haka kasar na a sahun gaba sosai a nahiyar Afrika wajen samar da cigaban fasahar ta zamani.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie