Pages

Games

Monday, 6 November 2017

Real Madrid ta huce haushinta a kan Las Palmas



Marco Asensio ya ci daya daga cikin kwallaye mafi bajinta a gasar La Liga ta bana, yayin da kungiyarsa Real Madrid ta wartsake daga kayen da ta sha a hannun Tottenham, inda ta buge Las Palmas.
Zuwa yanzu Real ba ta nuna bajintar da ta kai ta bara ba, wadda ta sanya ta yin karko, sai dai wasansu na ranar Lahadi ya fi wanda suka yi cikin tsakiyar makon jiya.
Cin da Casemiro ya yi da ka ne, ya sa Real Madrid ta yi wa abokiyar karawarta zarra, kafin Asensio ya dirka kwallon da ta kwantar da hankalin kungiyar daga ratar yadi 30.

Sai kwallon da Isco ya cafa, wadda ta kammale nasarar Real.
An ga Cristiano Ronaldo, wanda ya sa kwallon da aka ci ta uku, ya harzuka a cikin fili saboda karancin damammakin cin kwallon da ya samu, ko da yake, ya je daf da gola Raul Lizoain inda ya dankara kwallon da ta bude tsawon inci da dama ta fita.

Real Madrid ta yi kokarin kai hari sau 14 a farkon rabin lokaci, sai dai ba ta ci kwallo ba sai wadda Casemiro ya sa wa kai bayan an kwaso kwanar da Jonathan Calleri cikin rashin sani ya goga.
Yanzu dai kungiyar ce ta uku a kan tebur, inda suke kai da kai wajen maki da ta hudu Atletico Madrid, kuma jagorar gasar, Barcelona mai maki 31 ta ba ta ratar maki takwas.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie