Wani hoton da ya bulla a dandalin zumunta a satin da ya gabata na ci gaba da daukar hankulan jama'a da dama na Jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa Halima Atete da kuma tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a filin jirgi. Hoton dai na kunshe ne da jarumar zaune a kusa da shahararren dan siyasar inda ta dora wata jar hula da ke nuna alamun mubayi'a ga bin tafarkin Kwankwasiyya karkashin jagorancin tsohon Gwamnan. NAIJ.com dai ta samu daga majiyoyi da dama cewa an dauki hoton ne a filin sauka da tashin jirage na kasa-da-kasa dake a garin Dubai a dunkulalliyar Daular Larabawa. Da ma dai ba tun yauba jaruman dake shirya fina-finai a jihar ta Kano din suna nuna matukar kaunar su ga tsohon Gwamnan da suke kallon yana maraba da sana'ar ta su.
Source-: NaijHausa
No comments
Post a Comment