Pages

Games

Friday, 3 November 2017

Maryam Booth Tana neman tsari daga mutanen banza




Jarumar ta bayyana wasu haleyyan mutumin banza a shafin ta na kafar sadarwa tare da yin adduar neman tsari daga samun mutane irin haka a rayuwar ta Fitacciyar jaruma kuma mai Tauraro Maryam Booth tana neman tsari daga mutanen banza wadanda basu tsinana wa mutum komai kuma basu taimaka kawa wajen samun cigaba. "Mutumin banza shine wanda idan ya fusata da kai sai ya manta da matsayin ka. Kuma idanuwan shi su rufe ya dunga tona asirin ka. Ya manta da duk wata huldar arziki da aka yi dashi, har ma ya dinga fadar abun da babu shi a tare da kai na kazafi" ta wallafa a shafin ta. Daga karshe ta roki Allah ya nisantar da ita da samun mutanen banza a rayuwar ta. "Na roki Allah ya nisantar dani da samun mutanen banza a rayuwa ta kuma na rasa abokai da dama. "Ya Allah ka kara nisantar dani da ire-iren su" kamar yanda ta rubuta a harshen turanci. Suma masoyan ta sun tofa albarkacin bakin su a seshen tsokaci na shafin ta dangane da adduar da tayi inda yawacin su suka mata godiya tare da kara yin adduar neman kariya.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie