Games
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - abtechcomng@gmail.com
Wednesday, 1 November 2017
Kannywood: Jaruma Aisha Tsamiya Ta Sharara Karya A Bainar Jama’a
A cikin wani lamari mai matukar kunya da dariya, an bankado jirgin fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood mai suna Ai’sha Aliyu da aka fi sani da Tsamiya inda aka gano cewar jarumar ta sharara karya ne kawai a bainar jama’a a cikin wani shiri na gidan Talabijin na Arewa24.
Mun samu dai cewa a kwanan baya ne
jarumar ta sanar da samun gurbin karatun ta a budaddiyar jami’ar nan ta gwamnatin tarayya da ake yiwa lakabi da National Open University (NOUN) a turance domin ta yi karatun kimiyyar lafiya watau Health Technology.
NAIJ.com amma ta samu daga majiyar mu cewa ba a yin wannan kwas din a jami’ar kamar dai yadda Daraktan Watsa Labarai na jami’ar, Malam Ibrahim Sheme, ya fada wa majiyar ta mu.
Da yake karin haske, jami’in yada labarai na jami’ar ya kuma bayyana cewa watakila dai jarumar na so ne ta cewa Public Health don kuwa shine kadai kwas din da jami’ar
ke koyarwa da ya danganci lafiya.
Daga nan ne kuma sai ya jinjinawa jarumar game da yadda take da zummar yin karatu ba kamar sauran wasu matan ba.
What Others Are Reading
loading...
Copy the link below and Share with your Friends:
About Abtech Blog
Abtech.com.ng Is A Top Tech Blog That Provides Free And Cheap Browsing Cheats, Latest Phone And PC Updates,Blogging And SEO Tips, Tweaks And Tech News.
Abtech.com.ng Is A Top Tech Blog That Provides Free And Cheap Browsing Cheats, Latest Phone And PC Updates,Blogging And SEO Tips, Tweaks And Tech News.
By Haruna Lawan Usman on November 01, 2017
Labels:
Kannywood
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Designed With &
By Abijah Johnnie
No comments
Post a Comment