Nafisa Abdullahi ta yi zarra a Kannywood
- Nafisa Abdullahi ta lashe kyautar gwarzuwar Hausa Fim na shekarar 2017
- Ali Nuhu, Ramadan Booth sun halarci taron a Landan
Fitacciyar jarumar wasan Hausa Fim, Nafisa Abdullahi ta lashe kyautar gwarzuwar Hausa Fim na shekarar 2017 a bikin bada kyautuka na finafinan Afirka daya gudana a kasar Ingila.
An gudanar da wannan gagarumin biki ne a ranar Asabar, a birnin Landan, inda daga cikin wadanda suka halarci bikin karramawar har da Ali Nuhu da Ramadan Booth, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Ita ma jarumar tayi farin ciki sosai, inda ta bayyana hakan a shafin Twitter.
KU KARANTA: 2019: Matuƙar Buhari ba zai tsaya takara ba, toh ni zan tsaya – Yariman Bakura
Nafisa ta taka rawar gani a wasu fina finan Kannywood da suka hada da ‘Guguwar So’, ‘Dan marayan Zaki’ da ‘Ya daga Allah.’, kuma ta yaba da amsar wannan kyauta, duk da dai ba shi ne na farko ko na biyu ba, inji ta.
Nafisa Abdullahi
“Dayake dai wannan kyautr ba itace ta farko, ko na biyu, ko na uku a waje na ba, amma dai nayi matukar farin cikin (African Film Awards). Na sadaukar da shi ga duk wadanda suka taimaka min.”
In ji ta.
Nafisa tare da Ali Nuhu a Stamford Bridge
Daga karshe ta gode ma masoyanta, saboda goyon bayan da suke bata a kullu yaumin, sa'annan tare da ALi Nuhu suka garzaya filin wasan Chelsea na Stamford Bridge, inda suka kalli wasan Chelsea da Manchester.
No comments
Post a Comment