Pages

Games

Saturday, 28 October 2017

KADAN YA RAGE A DAMBACE TSAKANIN ABIDA MOH'D DA RASHEEDA MAI SA'A

DUK da cewar taron kungiyar mata masu aure ’yan fim da aka yi a Kano kwanan nan an yi shi an gama lafiya, sai dai kadan ya rage a dambace tsakanin Abida Mohammed da Rasheeda Adamu Abdullahi. A gaskiya, ba don shiga tsakani da aka yi ba, aka shawon kan su, to da kyar da tuni labari ya canza. Lamarin dai ya auku ne bayan an tashi daga taron. A daidai lokacin da mutane su ke fitowa daga wajen, sai kawai aka ji hayaniya ta kaure tsakanin jaruman biyu, wadanda a can baya aminan juna ne da ko barci ba ya raba su. Babu dai wata cikakkiyar magana a game da abin da ya hada su fada a wajen, amma dai a lokacin da Rasheeda ta ke fitowa daga dakin taron an ji ta ta na fada tare da yarfar da habaici ba tare da an san ko da wa ta ke ba. Amma fitowar Abida da kuma yadda su ka shiga fada wa juna bakaken maganganu shi ne ya sa aka fahimci inda maganar Rasheeda ta dosa. Sun shafe tsawon kusan minti 30 su na ta cacar baki da gori da tonon silili a tsakanin su, har ma da kokarin kai wa juna duka. Abida ce ta fi zakewa a wajen kai dukan, ana ta rirrike ta, yayin da ita kuma Rasheeda aka yi kokarin saka ta a motar ta. Hakan bai sa Abida ta janye kudirin ta na kai wa Rasheeda duka ba. Jama'a sun cika wajen, ciki har da masu wucewa, su ka tsaya su na kallo. Abin dai babu tsari, sai wanda ya gani! An samu shawo kan fadan ne a lokacin da Saima Mohammed ta fito daga dakin taron, ta ga abin da ya ke faruwa, don haka ta je ta shiga tsakin su. Ganin girman ta ne ya sa Rasheeda ta ja motar ta, ta bar wajen, yayin da ita kuma Abida aka janye ta da karfin tsiya.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie