Pages

Games

Saturday, 28 October 2017

Honarable Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice

Fitaccen dan majalisar wakillan nan na Najeriya mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, 'Yankwashi da kuma Gwiwa dukkan su a jihar Jigawa dake a Arewa maso yammacin Najeriya mai suna Honarable Muhammad Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice.
Shahararren dan majalisar dai ya yi wannan caccakar ne a yayin da yake tsokaci a zauren na majalisar game da sabon tsarin nan na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari din da ke fitar da doyar da aka noma zuwa kasashen ketare.
Hausazone.com dai ta samu cewa ta yake tsokacin, Alhaji Gudaji Kazaure ya nuna rashin dubara da kuma sanin ya kamata daga bangaren gwamnatin game da wannan tsarin inda yace shi baiga yadda za'ayi talaka ya mori wannan irin bahagon tsarin ba na fitar da kayan abinci zuwa kasashen waje sannan kuma an hana shigowa da shi.
Dan majalisar daga karshe sai ya jawo hankanin shugabannin majalisar yan uwansa da ma sauran shugabannin kasar a dukkan matakan mulki da su duba wannan matsala domin kawo gyara.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie