Pages

Games

Thursday, 12 October 2017

Dandalin Kannywood: Har yanzu da sauran kuruciya ta - Rukayya Dawayya


Fitacciyar jarumar nan tsohuwar fuska a fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood watau Rukayya Dawayya ta fito tayi fatali da kiraye-kirayen da jama'a ke yi mata na ta yi aure inda tace ita fa har yanzu yarinya ce karama. Shahararriyar jarumar da ta taka muyimmiyar rawa a fina-finai da dama tare kuma da bada gudummuwar ta musamman ma wajen habakar masana'antar ta ayyana cewa ita duka-duka yanzu shekarar ta 29 a duniya.
Majiyarmu a cikin wani dan nazari da tayi game da zancen nata ta binciko cewa indai har hakan ta tabbata to lallai kenan jarumar tana da shekaru 13 kacal a duniya ne ta fito a cikin fim din Dawayya.
Shi dai fim din Dawayya kamar yadda binciken namu ya tabbatar, an shirya shi ne a shekara ta 2001 wanda yanzu kimanin shekaru 16 kenan. A lissafi kenan idan aka cire shekaru 16 daga cikin 29 ya zama shekaru 13.

Naijhausa

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie