Games
For Questions, Inquiries, Click Here
Page | Group - Follow us - Call us - Hire Us - abtechcomng@gmail.com
Sunday, 8 October 2017
Hadakar Kungiyoyi 72 Ne Ke Kiran Gwamnati Ta Dakile Yawan Hare-haren da Boko Haram Ke Kaiwa a Borno
Kungiyoyin matasa na maza da mata suka yi gangamin kiran gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen dakile yawan hare-haren da 'yan Boko Haram ke kaiwa koina a jihar Borno musamman a kewayen manyan garuruwa kamar Maiduguri
Wasu kungiyoyin matasa dake neman zaman lafiya a Jihar Borno sun kira gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen dakile yawan hare-haren da ‘yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa cikin jihar Borno.
Kungiyoyin su 72 sun yi kiran ne a lokacin wani taron gangami da suka shirya cikin garin Maiduguri, inda suka yaba da aikin da sojojin Najeriya ke yi amma suka nuna cewa har yanzu ana samun hare-hare irin na sari ka noke nan da can musamman a bayan gari.
Alhaji Babagana Gambo, shugaban hadakar kungiyoyin, ya shaidawa wakilinmu Haruna Dauda cewa sunyi kiran ne ganin cewa duk da yakin da ake yi da kungiyar, hare-haren sun ki karewa.
A bangaren mata kuma, Hajiya Yagana Alkali, shugabar matan, tace rikicin ya fi shafar mata, inda take nuni da mata da yawa da aka kashe mazajensu,
wadanda ke cikin kunci saboda an barsu da yara. Akwai kuma yara da dama da basu iya ci gaba da makaranta. ‘Yan mata kuma da suka balaga wasu na yin lalata dasu yayinda suka fita daga sansanin ‘yan gudun hijira domin neman abun da zasu ci.
A cewar Hajiya Yagana, mata fiye da dubu arba’in ne yanzu suka rasa mazajensu sakamakon rikicin Boko Haram kana ‘yan mata kimanin dubu biyar ne suka yi ciki
What Others Are Reading
loading...
Copy the link below and Share with your Friends:
About Abtech Blog
Abtech.com.ng Is A Top Tech Blog That Provides Free And Cheap Browsing Cheats, Latest Phone And PC Updates,Blogging And SEO Tips, Tweaks And Tech News.
Abtech.com.ng Is A Top Tech Blog That Provides Free And Cheap Browsing Cheats, Latest Phone And PC Updates,Blogging And SEO Tips, Tweaks And Tech News.
By Haruna Lawan Usman on October 08, 2017
Labels:
Labarai
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Designed With &
By Abijah Johnnie
No comments
Post a Comment