Pages

Games

Sunday, 8 October 2017

Hadarin Kwale-kwale a Jihar Kebbi Ya Kashe Mutane Bakwai, Wasu da Dama Kuma Sun Bace



Cikin 'yan kwanakin nana Jihar Kebbi na fama da yawan hadarin kwale kwale dake cinye rayukan jama'a kamar na ranar Lahadi shi ne na hudu shi ma ya hallaka mutane bakwai tare da bacewar wasu
Hadarin kwale-kwale na baya bayan nan da yayi sanadiyar mutuwar mutane bakwai tare da bacewar wasu da dama shi ne na hudu a jihar a cikin ‘yan kwanakin nan.

A zantawar da yayi da wailinmu Murtala Faruk Sanyinna, Alhaji Sani Dododo shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa (SEMA) a jihar Kebbi, ya tabbatar da hadarin na jiya da yamma kuma ya fadi wasu daga cikin dalilan dake janyo irin wadanan haduran a yankin.
Alhaji Sani Dododo ce akwai ruwa da akan sako daga madatsar ruwa da yawan ruwan sama da ake samu, da daukan mutane fiye da kima da jiragen keyi tare da mugun gudu da ganganci da matukan jiragen ke yi.

Ya kira masu tuka jiragen da kungiyoyinsu da hukumomi su kula da yadda ake daukan fasinjoji da kuma yin la’akari da yanayin da ake ciki domin a kiyaye rayukan mutane.
A kan yadda za’a shawo kan matsalar Alhaji Sani Dododo yace hukuma zata kayyade adadin fasinjojin da kowane jirgi ya kamata ya dauka. Haka ma an hana kowane jirgi tashi bayan karfe biyar na yamma.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie