Garin Da Mata Ke Rokon Maza Su Lakada Musu Tsinannen Duka A Matsayin Tsantsar Soyayya.
Fassarar Maje El-Hajeej Hotoro
'Yan kabilar Hamar a kasar Ethiopia sun yarda farfasawa Mace jiki da duka alama ce ta nuna tsananin soyayya a gareta. A wata Al'adar auren su mai suna Ukuli Bula da suke gudanarwa a matsayin bikin nuna soyayya Mace ta kan roki Namiji a bainar jama'a ya rika zabga mata bulala ta na rawa tana waka a matsayin hanyar hanyar bayyana masa tsagwaron soyayya da aminci. Shi kuma Namijin da ya yi dukan wannan ne zai bayyana ya cika Namiji sai a amince masa ya yi aure.
No comments
Post a Comment