Addu'a Idan Mai Azumi Zai Buda Baki
ذَهَبَ الظَّمَأُ، وَابْتَلَّتِ العُرُوقِ، وَثَبَتَ اْلأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللهُ.
Zahabaz-zama-o wabtallatil-'urooq, wathabatal- ajru in shaal-lah.
Kishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah Ya so.
Abdullahi bn Amr bn Al-As ya ce Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Mai azumi yana da addu'a da ba a mayar da ita idan ya zo bude baki". Abdullahi bn Amr ya kasance idan ya zo buda baki sai ya ce;
اللّهُمَّ إِنَّي أَسْأَلُكَ بِرَحْمَتِكَ الّتي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْءٍ، أَنْ تَغْفِرَ لِي .
Allahumma inne as-aluka birahmatikal-latee wasi'at kulla shay'i, an taghfira lee.
Ya Allah! Ina rokon Ka saboda Rahamarka da ta yalwaci komai, Ka gafarta mini.
No comments
Post a Comment