Pages

Games

Monday 24 July 2017

Gwamnan jihar Imo ta Nigeria Rochas Okorocha ya ce sun dauki kimanin sa'a guda suna cin liyafa tare da shugaban kasar a bayyanarsa ta farko a bainar jama'a tun bayan da ya tafi jinya a birnin London kwanaki 78 da suka gabata.
Mr. Okorocha dai na daya daga cikin gwamnonin jam'iyya mai mulki ta APC 4 da suka ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a inda yake jinyar, tare da Shugaban Jam'iyyar na kasa Cif John Oyegun da Ministan Sufuri Rotimi Ameach ranar Lahadi.
Sauran gwamnonin da ke cikin tawagar sun hada da Umar Tanko Almakura na jihar Nasarawa, da Nasir Elrufai na jihar Kaduna da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar dangane da wannan ganawar, mai ba shugaban shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya ambato Gwamna Rochas Okorocha na cewa shugaban na cike da annashuwa kuma har yanzu yana nan da halayyarsa ta yin raha da mutane.
Gwamnan ya ce tawagar tasu ta dauki kimanin sa'a daya tana liyafa tare da shugaban kasar, kuma inji shi daga tattaunawar da suka yi ga dukkan alamu yana sane da dukkan abubuwan da ke faruwa a gida Nigeria.
Mr. Okorocha ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa da ziyarar tasu kuma ya tambayi ko wnane daga cikin gwamnonin abin da ke faruwa a jiharsa.
An yi wa Shugaba Buhari addu'o'i a Guinea
Yaushe rabon Buhari da Nigeria?
'Muna sa ran dawowar Buhari nan ba da jimawa ba'
Sanarwar ta ce da suka nemi jin abin da zai ce game da suka da miyagun kalaman da wasu 'yan kasar ke furtawa game da halin da yake cikin, sai ya yi dariya kawai tare da bayyana abubuwan da ake fadan a zaman karairayi, ya kara da cewa abin da shugaban ke jira kawai shi ne likitocinsa su bashi dama ya dawo gida.
Hoton da fadar shugaban ta saka a shafinta na Twitter dai ya nuna shi sanye da jamfa da wando bakake, da shudiyar hula, da kuma farin tabarau; yana murmushi a gaban wani teburi da aka jera wa abubuwan sha da kuma ayaba.
Ziyarar gwamnonin dai na zuwa ne kwanaki 12 bayan da mataimakinsa - wanda ya bar wa rikon kasar - ya kai masa wata gajeruwar ziyarar kuma ya shaida wa al'ummar kasar cewa mai gidan nasa na samun sauki cikin sauri kuma zai dawo kasar ba da jimawa ba.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie