-Masu son rikici ta barke su ke mara ma Kanu baya
-Nayi tafiya da ga arewa zauwa kudu da neman neman hadin kan yan Najeriya
-Da ace matasan Arewa sun mai da martani zuwa ga Kanu ko IPOB da nace sunyi adalci
Babban jam’in tsaron na tsohon shugaban kasan Najeriya janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yace wasu mutane suna kashe makudan kudade akan shugaban kungiyan neman yanci Byafara IPOB, Nnamdi Kanu dan raba Najeriya.
Al-Mustapha yace jami,an tsaro suna iya kokarin tona asirin mutanen.
Ya gaya ma yan jaridan Vanguard cewa “ana shi fahimtar akwai wasu da ke kashe kudaden su saboda matsalan yaci gaba da habbaka dan biyan bukatan kansu, amma jami’an tsaro suna iya kokarin tona musu asiri.
Byafara: An kusa tona asirin wa'yanda suke kashe makudan kudade akan Kanu-Almustapha
Duk wani kira dan ake yi dan araba kasannan ba a yarda da shi ba. Ina iya kokari na dan ganin hadin kan yan Najeriya. Na yi tafiya zuwa sassan kasan daban daban daga Arewa har zuwa kudu, da kuma Magana da duk wani mai ruwa da tsaki dan samun zaman lafiya da hadin kan yan kasa.
Idan ace matasan Arewa sun maida da martani ne zuwa ga kungiyan IPOB ko shugabansu Nnamdi Kanu da zance sunyi adalci, amma suce gaba daya iyamurai su tattara su bar jahohin Arewa basu kyauta ba kuma yin haka ya sabawa dokar kasa.
“Mun tattauna da shuwabannin kungiyan Arewa da kuma Ralph Unwazureuike saboda Nnamdi Kanu yaron shine kuma shi yakawo shi gidan Rediyon Landan.
“Masu son rikici ta barke a kasanan su ke mara wa Kanu baya. Ba lallai dan rikici ya keyi abun da yakeyi ba, amma wa’yanda suke mara mishi baya su ke son rikici ya auku saboda araba
No comments
Post a Comment