Pages

Games

Tuesday, 11 July 2017

Labari da dumi duminsa

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya garzaya birnin London domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.
Wata takaitacciyar sanarwa da kakakin mukaddashin shugaban kasar Laolu Akande ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce Farfesa Osinbajo zai tafi London ne a ranar Talata.
Sanarwar ta kara da cewa, "Mukaddashin Shugaba Osinbajo zai gana da Shugaba Buhari a London a yau (Talata), sannan zai dawo Abuja da zarar sun kammala ganawa".
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa Shugaba Buhari ne ya bukaci mukaddashin shugaban kasar ya je wurinsa domin su tattauna kan wasu batutuwa.
Dole Buhari da Osinbajo su bayyana sunayen 'barayi'
'Yan majalisa sun dakatar da nadin mukaman da Osinbajo ya aika
Shugaba Buhari ya kwashe sama da wata biyu a birnin London inda yake jinya.
Wannan dai shi ne karo na farko da mutanen biyu za su gana tun da shugaban na Najeriya ya fice daga kasar.
A watan Maris ne ya dawo daga hutun jinya na mako bakwai a Birtaniya, sannan ya koma a watan Mayu.
A lokacin da ya dawo daga London, Shugaba Buhari ya ce bai taba yin rashin lafiya irin wacce ya kwanta ba.
Ya ce an kara masa jini ko da yake bai fadi cutar da ke damunsa ba.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017
19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
Shin fitowar Buhari za ta sauya al'amura a Nigeria?

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie