Pages

Games

Wednesday 23 August 2017

Ba Zan Taba Mancewa Da Halaccin Da Kwankwaso Ya Yi Min Ba, Inji Shugaban Kwankwasiyya Nigeria, Ali Artwork

GABATARWA:
Sunana Ali Muhammad Idris, wanda aka fi sani da ALI ARTWOK. an haife ni a unguwa uku , karamar hukumar tarauni. jihar kano. 1st, january, 1992. na fara karatun firamari a unguwa uku special primary school a 1999 zuwa 2005. bayan nan na wuce kai tsaye Government junior school unguwa uku. a shekarar 2005 to 2008, bayan na gama junior sec school dina, na wuce babbar sakandire ta gwamnati dake KUNDILA. (GSS KUNDILA). na fara ta a shekarar 2008, to 2011. daga nan na fara karatun NCE a makarantar sa'adatu rimi collage of education kumbutso. a cikin garin kano. na yi karatun yare na ENGLISH da HAUSA. saboda matsalar kudi na ajiye karatuna na bayan na je NCE 2, daga nan na tsinci kaina a sana'o'i da dama kamar DAKO, DINKI, ZANE, EDITING sannan na fara ACTING comedy da sauran su, godiya ga ALLAH da nayi wadannan abubuwan dana lissafa. duk da naga fafatawa kala kala a hanyar tsira da rayuwata. sannan naga nasarori dana samu a rayuwata. na samu kambun karramawa na gasar MTN 2016 da akayi a ABUJA, a bangaren wanda yafi kowa iya editing. sannan na sake cin nasara a gasar AMMA awards, a matsayin wanda yafi kowa iya shirya tallar fina finai. na samu kambun karramawa na arewa creative industry a jihar kaduna nigeria. nasarori da yawa suka ci gaba da budowa a rayuwata, har na bude kamfanin MUSHA DARIYA (AREWA COMEDIANS) saboda ina yin comedy. shi yasa na fara kananan video na comedy. harta kai ga ina da websites da mutane ke rububin shiga dan kallon comedies dina a dukkan fadin duniya. Sannan ni na kafa kungiyar magoya bayan SANATOR ENGR. DR. RABI'U MUSA KWANKWASO, wato (KWANKWASIYYA NIGERIA).
DAILY TRUST: Zamu so sanin cikakken dalilin daya sa ka bude kungiyar kwankwasiyya nigeria.
DALILIN KAFA KUNGIYAR:
ARTWORK: Ni mutum ne dake girmama alkhairi ko karamci ko yaya yake, wannan ne yasa ba zan taba manta karamcin da mai girma SANATOR ENGR. DR. RABIU MUSA KWANKWASO yayi mana ba, a shekarar 1999, lokacin dana shiga primary school. lokacin maganar gaskiya mahaifina bashi da lafiya, ya shafe shekaru biyar ko fita baya yi. inda mahaifiyata ce ta kokarta ganin nayi karatun. kasan dalibi kuma yaro karami bashi da burin daya wuce kudin tara, littafai da sauran abubuwan da zasu amfaneshi a makaranta. da fargabar haka na fara karatun, cikin ikon Allah sai tallafin Sanator Engr. DR. Rabiu musa kwankaso a lokacin yana kujerar gwamna a jihar kano, ta fado kanmu. ya dauke mana dukkan wannan dawainiyar mu da iyayenmu. karatu kyauta, abinci kyauta, takardu da kayayyakin makaranta, hatta uniform shima kyauta. wanda nasan duk wanda yake a kano yasan da haka a kano a lokacin. to a takaici dai ni akansa na fara sanin taimako irin haka akaina, saboda haka na taso na rayu da sonsa a raina saboda yayi min wani abu da bazai taba yiwuwa na manta dashi ba. musamman bamu yi nisa ba muka gane banbancin sa da sauran 'yan siyasa.
DAILY TRUST: Menene banbancin da ka tsinta wanda ba a yi nisa ba tsakaninsa da sauran 'yan siyasa?
ARTWORK: muna kammala karatun primary da gata da jin dadi saboda tallafin da mai girma gwamnan kano ya bamu. muka tunkari makarantar gaba da primary wato secondary. Ni a kaina na fada makarantar ne cike da zaton samun gata irin wadda aka yi mana a primary, sai dai taku kadan da shigata na fahimci mafarki nake. saboda ba karamar wuya nasha ba, bani kadai ba, dukkan dalibai irina munji wuya saboda babu wani tallafi da muka samu koda rabin irin na gwamnatin data wuce ne. dan ni dakyar ma na samu na kammala karatun... a dalilin haka yasa na fadi jarabawa. saboda ba abu mai sauki bane kaji da abu biyu a gabanka a lokacin. ga karatu, ga tunanin hanyar biyan karatun, ga bukatar gida, ga matsalar iyaye. kaga kuwa dole mutum ya fadi. na samu credit biyu da pass, english da islamic studies. sai sauran dukka pass. bayan mun gama haye wannan siradin dakyar, mun kammala makarantar sakandire 2011 a hakan ina gumurzu ne fa, da fadi tashi na samu na fada Sa'adatu Rimi collage of education.
DAILY TRUST: Daka tsinci kanka a makarantar gaba da sakandire wane banbanbanci ka samu dana baya, akwai ci gaba koko ka samu wani tallafin kamar na lokacin gwamnatin kwankwaso?
ARTWORK: (Dariya) wane tallafi? ai jikina ne ya fada min, saboda da gumi na, da gumurzun zuwa wurin koyon aiki na samu na lallaba na mallaki wasu kudade adadin dubu sha hudu, na kai makaranta aka bani free NCE. na fara muka cinye shekara daya dakyar da gumi. muka shiga ta biyu, muna rarrafawa wato NCE 1. azaba da fadi tashin dana sha babu wani tallafi sai dai daga Allah, yasa kafafuna suka sare na kife. naji taifyar karatun tunda babu irin su kwankwaso a duniya a lokacin bazai yiwu min ba. na jingine karatun gefe guda. dan tafiya a kwale kwalen da ya huje a tsakiyar teku barinta yafi daidai, in ba haka ba sai ka dulmiye gaba daya.
DAILY TRUST: Ka bar karatun dan bazaka iya ba, to kana jiran irinsu kwankwaso su dawo ne, koko wane dalili ne?
ARTWORK: Saboda dai in samu damar da zan ci gaba da koyon aiki. wanda watakila a cikinsa na samu damar ci gaba da karatun... daga nan naci gaba da fadi tashina har na fara samun nasarori, amma fa kada ka manta soyayyar kwankwaso na cikin raina saboda lokacinsa ne kadai a lokutan rayuwata dana san dadin karatu, kuma kullum shi masa albarka nake, saboda yayi min wani abu mai girma a rayuwata. kwatsam sai ya sake bayyana zaiyi mulki. sai naji kamar ni Allah ya amsawa addu'a ya sa kwankwaso ya dawo. ya samu nasarar sake hayewa kujerar gwamnatin kano a shekarar 2011.
DAILY TRUST: To da ya dawo ka samu wani tallafi ne, irin wanda ya taba baka a baya?
ARTWORK: Ban san inda zan ganshi ba, amma dai ina sonsa ni da gaske a raina, sai kuma ikon Allah yasa abinda nasan shi wato tallafawa talakawa ya karu. ya dauki nauyin karatun mafi yawancin talakawan da suke karatun saboda shi zuciyar sa ta taimako ce ga marasa karfi. sannan yayi maganin ta'addanci daya fitini jihar a lokacin, saboda yasan talakawa ne abin ke cutarwa. ta hanyar nemawa talakawa aiki, musamman matasa maza da mata aikin yi. wanda har saida ya gama mulkinsa, ba a kara sara suka ko ta'addanci ba. tunda sun samu abin da zasu rike kansu. sannan ya sayi motoci masu tsadar gaske dan yaran talakawa karatunsu ya saukaka. sannan abunda kowa da ya taba ziyarar kano ada da yanzu zai iya ganin banbanci shine gyaran da yayiwa kano da gadoji dan saukaka cunkoso, ga fitilu dan inganta garin kano. kaga ko wannan abun dole ya kara min sonsa dan bai bani kunya ba. a daidai wannan lokacin ni kuma nasarori suka tunkaro ni. musamman ta hanyar wasannin barkwanci, sanin da aka yi min, sai naga yanzu ne ya kamata na bayyanawa duniya soyayyata ga Sanator. Engr. Dr. Rabiu musa kwankwaso. sai naci gaba badan wani ko wata ba, sai dan son da nake masa. babu faragaba dan nasan duk abinda zan fada haka yake duniya ma ta sani, ba shaci fadi bane dan birgewa saidan tunawa duniya jarumtar da yayi.
DAILY TRUST: Wadanne hanyoyi ka bi da har kungiyar taku ta zama kungiya? musamman lokaci daya ta sanu a bainar jama'a.
ARTWORK: Ni da yayana mai suna ENGR. SAMA'ILA MUHAMMAD IDRIS muka fara zama muka fara tattaunawa da tsara komai wanda aka yanzu haka ya gama karatu a BAYERO UNIVERSITY. yanzu haka yana bautar kasa a jihar BAUCHI, mataki na farko dana fara bi shine shawarawari bayan na gamsu, sai na tunkari wani lauya a kano BARISTA SIDI, tare da sanar dashi kudirina, yayi min kokarin abubuwan da ni ban sansu akan kungiya ba a lokacin, rijistar kungiya na biya. da sauran dukkan abubuwan da suka dace da yayimin. bayan haka, sai na zauna na tsara logo na kwankwasiyya bayan gama rijistar kungiya da muka yi. muka bude shafuka dan yada manufofin mu. a instagram, twitter, facebook da website. wanda a yanzu haka muke aikinsa bamu kai ga gamawa ba.
DAILY TRUST: Har yanzu bamu ji shin ko sanator yasan da zaman ku ba, ko kuma yaya mu'amalar ku da shi ta fara?
ARTWORK: Ina ci gaba da gabatar da al'amura na ba tare da tunanin wani ba saboda soyayya ce a raina, kwatsam yaronsa MUBARAK KWANKWASO yayi min magana a DM wato a instagram yace in bashi number ta zaiyi magana dani. kaga wannan ma nasara ce, saboda yadda yaga muna ta posting a yanar gizo da yada abubuwan mahaifinsa sai abin ya birge shi, har yasa ya nemi lambata. bayan na bashi ya kira ni mun dade muna tattaunawa a kai, shin mahaifinsa ya san dani? nace masa a'a dan ban taba ganinsa ba. wannan ne mataki na farko na haduwar mu da mahaifinsa. ya hada ni da odilin mahaifinsa mai suna LITI. akan mu gabatar da kanmu. kuma cikin ikon Allah komai yazo da nasara. muka ganshi yasan damu, muka tattauna sosai.
DAILY TRUST: Haduwar ku dashi ta kara maka haske ga halayyarsa koko baka ganshi yadda kayi zato ba?
ARTWORK: Na sha mamaki, saboda mutum ne daya amshe mu da fara'a da faran faran kamar yadda yaronsa ya yi min. muka tattauna tare da samun kwarin guiwa a wurinsa, ya yaba mana matuka, sannan yaja kunnen mu akan muyi komai akan tsari da girmamawa ba tare da cin mutumcin wani ba.
DAILY TRUST: Akwai wadanda zasu yi maka kallon kana wahalar da kanka kana bata lokaci akan siyasa, shin yaya kayi da wannan?
ARTWORK: Dukkan tafiya ta rayuwa ta kumshi haka, akwai masu yabonka da baka gwarin guiwa a dukkan abunda zaka yi na alkhairi, sannan a gefe guda akwai masu ganin shirme kake da zaginka. a cikin tafiyar nan na samu matsalar wasu daga ciki, wadanda basu fahimci dalilin tafiyar ba kwatakwata. su sun saba suje wurin 'yan siyasa suyi roko dan a basu wani abu, mu kuma tafiyar mu ta kwankwasiyya tafiya ce tsarkakakkiya da zata nuna muhimmanci da ci gaban al'umma. tun a nan muka raba hanya da su. ina so inja hankalin jama'a akan siyasa, ya kamata mu daina siyasa ta kudi, ko kwadayi. muyi ta kishi da son mai son ci gaban al'umma ta wannan hanyar ce kadai nake tunanin za'a iya gyara siyasar najeriya. musamman yadda kwankwaso ya zama zakaran gwajin dafi a cikin 'yan siyasa
DAILY TRUST: Wane banbanci ne a zahiri da yake banbanta kwankwaso da sauran 'yan siyasa da kake fada?
ARTWORK: Kasan ita siyasa manufarta, shine a taimaki al'umma, amma wasu daga cikin 'ya siyasa shine suci daga al'umma. mutum ne zaka ga an zabe shi baya iya cika alkawarin daya dauka ga al'ummar da suke zabe shi. banbancinsa da su shine, shi duk abunda zai fada yayi, har ma yazo ya ninka. akwai alkawarurrukan da bai yi yayi su. duk wani abu daya ga zai kawo ci gaban al'ummarsa sai da yayi shi. sannan ga kishin da yakewa al'ummarsa. wannan ma wani banbanci ne tsakaninsa da sauran 'yan siyasa. shi yasa nake fatan Allah yasa ya zama shugaban Kasa. 'yan najeriya zasu more da jin dadin mulki, daga kudu har arewaci.
DAILY TRUST: A matsayinka mai kishin ci gaban al'umma, wace shawara zaka ba sauran 'yan siyasa?
ARTWORK: Shawarata bata wuce kira ga 'yan siyasa da su zamanto masu taimakon al'ummar da suka zabe su, hakan ne zaisa a yi musu soyayyar da suke ganin ana yiwa kwankwaso tana birge su. in ka dauki majority na masoyan kwankwaso ba domin kudi suke sonsa ba, suna sonsa dan yana son ci gaban al'umma da kuma taimako a gare su.
DAILY TRUST: Mun gode
ARTWORK: Nima na gode.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie