Pages

Games

Thursday 24 August 2017

HATTARA: Kanjamau ya zama ruwan dare a Abuja – Likita Walter

Shugaban wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Civil Society For HIV and AIDS in Nigeria’ Walter Ugwocha ya ce mazauna babban birnin tarayya, Abuja za su iya fadawa matsalar yawan kamuwa da cutar kanjamau.
Ya fadi hakan ne a lokacin da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi hira da shi a makon da ya gabata.
Walter Ugwocha ya ce adadin yawan mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a cikin garin Abuja sun kai kashi 7.5 bisa 100 sannan kauyuka kamar su Mpape na da mutane masu yawa da ke dauke da cutar.
Da ya ke sanar da PREMIUM TIMES bayanai akan yadda cutar ke yaduwa a garin Abuja, Walter ya ce sau da yawa za ka ga shugabanni a ma’aikatu da ke dauke da cutar ne suke yada shi ga kananan ma’aikata da ya hada da musamman sakatarorinsu da masu yi musu hidima a wajen aiki.
Shugabannin wanda magidanta ne suma sukan kwana da irin wadannan ma’aikata inda bayan haka sai suma su kamu da cutar. “ Idan kuma suka koma gidajensu sai su kwana da samarinsu. Ita kanta matan Oga a gida bayan ya sadu da ita, itama sai ta kwana da saurayinta idan mijin baya nan. Ta haka sai kaga cutar na ta yaduwa.”
Walter ya ce Unguwanni kamar su Mpape da Maraba ne aka fi samun irin wadannan mutane da suke yada wannan cuta saboda kamar yadda bincike ya nuna su wadannan kananan ma’aikata sun fi zama a irin wadannan unguwanni.
“ Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa mafi yawan mutanen da ke zama a Abuja na cikin hadari na kamuwa da cutar Kanjamau idan har ba a kiyaye ba.”
Da ga karshe ya ce mafi yawan mata a garin Abuja na aikata sana’ar Karuwanci saboda kudin da suke samu ba tare da la’akari da illar da ke cikin haka ba.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie