Pages

Games

Thursday, 24 August 2017

Wata cuta da ba a san ko wace iri ce ba ta Kashe mutane sama da 50 a jihar Kogi

Wata cuta da likitoci basu gane ko wace iri bace ta yi sanadiyar mutuwan mutane 50 a kauyukan Okunran, Okoloke da Isanlu-Esa dake karamar hukumar yammacin Yagba a jihar Kogi.
Alamomin kamuwa da cutar sun hada da amai da gudawa, zazzabi da dai sauransu.
Ma’aikaciyar asibitin ECWA dake Egbe Jannette Hathorn ta baiyana wa kwamishinan kiwon lafiya na jihar Saka Audu a lokacin da ya kawo musu ziyara cewa da farko suna zaton cutar zazzabin Lasa ce ta kama mutane amma bayan gwajin da suka yi sun gano ba haka bane.
“Wani mutum ya kawo dansa asibitin mu inda ya fada mana cewa mutane 50 sun rasu sanadiyyar kamuwa da cutar.”
Jannette Hathorn ta ce da jin hakan sai suka kira hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO domin su taimaka wajen gano ko wani irin cuta ce ta bullo musu.
” Ma’aikatan hukumar WHO sun zo sun dauki jinin marasa lafiya domin yin gwaji akai ko za a gano wace irin cuta ce.”
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Saka Audu ya ce gwamanti na iya kokarin ta wajen ganin ta hana yaduwar cutar musamman ga mazauna karkara.
Ya ce abu daya da suka sani shine cutar da ta bullo ba cutar zazzabin Lasa ba ce sannan sun dauki jinin mutanen dake dauke da cutar zuwa asibitin dake Irrua jihar Edo domin yin gwaji da gano ko wace irin cuta ce.
Bayan haka shugaban Fulani da ke zama a yankin Ardo Damina ya fadi wa manema labarai cewa cutar ta bullo a wurin su cikin makon da ta gabata ne kuma yara kanana ne suka fi kamuwa da ita.
Ya ce sun fara magance cutar da maganin gargajiya amma da abin ta gagara sai suka garzaya asibiti.
Ardo Damina ya ce sun shiga halin rudani bayan da likitoci suka kasa gane irin cutar.
” Mun rasa mutane sama da 50 sannan akwai sauran dake fama da cutar a gida.”

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie