Pages

Games

Thursday 31 August 2017

Dandalin Kannywood: Dukkan abun da kake bukatar ka sani game da mai zazzakar murya Ali Jita

Shi dai Ali Jita an haife shi ne a unguwar gyadi-gyadi a cikin badalar Kano dake a Arewacin Najeriya sannan kuma ya yayi karatun sa na Firamare da kuma Sakandare duk a birnin Ikko na jihar Legas a wata makarantar sojoji,


Dandalin Kannywood: Dukkan abun da kake bukatar ka sani game da mai zazzakar murya Ali Jita

 ta samu kuma cewa daga baya ne sai mawakin ya kuma dawo jihar Kano inda ya kammala karatun sa na Difloma akan harkar mulki da kuma a fannin na'ura mai kwakwalwa duk dai a Kano din.

Mawakin haka zalika binciken mu ya samu cewa ya tsunduma a harkar wake-waken Hausa ne a cikin shekara na 2009 a inda kuma nan da nan ya samu karbuwa a zukatan al'umma sakamakon kwarewar sa da kuma zazzakar muryar sa.

Mawakin dai yanzu haka ya samu nasarori da dama inda ya lashe kyaututtuka masu tarin yawa sannan kuma ya fitar da kundin wakoki da yawa.

Ka wo yanzu dai lokacin hada wannan rahoton, mawakin yana da auren sa mata daya kuma Allah ya albarkace su da samun ya'ya biyu. Haka zalika babban masoyin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ne

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie