A yau Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun yarjejeniya guda tara, ciki har da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ke da hedikwata a Dubai.
Gwamnatin Najeriya ta ce yarjejeniyar za ta karfafa yaki da cin hanci da rashawa, sannan kuma za ta inganta tattalin arziki da kuma matakan tsaro.
Daya daga cikin yarjeniyoyin su ne na tsarin mutunta juna wajen batun shari’a tsakanin kasashen biyu. Hakan na nufin cewa duk wanda ya saci kudi daga Najeriya ya gudu Dubai, to za a kamo shi a dawo da shi Najeriya. Haka kuma za a dawo wa Nijeriya da kudin da ya boye ko dukiyar da ya tara a can.
Dubai ya zama wani tudun-mun-tsira ga manyan barayin gwamnati, wadanda su ka yi kaka-gida a can.
Idan ba a manta ba, tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori can fara gudu ya yi zaman sa, a lokacin da Nijeriya da kasar Ingila su ke neman sa ruwa jallo.
Daga can ne jami’an tsaron Dubai su ka kama shi, aka tasa keyar sa zuwa Ingila, inda ya yi zaman kurkuku na hukuncin shekaru hudu.
Da ya ke bayani yayin bikin sa hannun yarjejeniyar, Buhari ya umarci dukkan hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki a sha’anin wannan yarjejeniya da su yi dukkan abin da ya dace wajen kiyaye wannan yarjejeniya.
Buhari ya ce an samu tsaikon fara amfani da yarjejeniyar ne saboda jiran kowane bangare daga Najeriya da UAE su kammala rattaba tsare-tsaren su na yarjejeniyar.
Sauran yarjeniyoyin sun hada da ta Tabkin Chadi wadda aka kulla tsakanin Najeriya, Kamaru, Afrika ta Tsakiya, Libya, Nijar da Chadi da kuma wasu yarjeniyoyi daban.
No comments
Post a Comment