Pages

Games

Tuesday, 20 June 2017

Labari da dumi duminsa

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da sabbin matakai guda tara da ta kara akan dokar shan taba sigar da aka zartar a shekarar 2015.
Ministan lafiya Isaac Adewole shi ya sanar da haka a taron wayar da kan jama’a a kan illolin da ke tattare da zukar taba sigari mai taken ‘Tobacco: A Threat to Development.’
Taron dai ana yin shi ne a kowacce shekara yayin da ranar kin shan taba sigari ta duniya ta zagayo.
Ministan ya ce nan ba da jimawa ba za a fara amfani da sabbin matakan da suka hada da:
1. Hana saye da sayarwar taba sigari ga duk wanda bai cika shekara 18 da haihuwa ba.
2. Hana siyar da sigari kara-kara. Sai dai a sayar da ita kwali kwali 3. Za a na sayar da sigari mara fitar da hayaki wanda nauyin shi bai kasance kasa da gram 30 ba.
4. Hana talla ko kuma siyar da sigari ta Email da yanar gizo.
5. Hana kamfanonin da ke sarrafa sigari tsoma baki a batutuwan da suka shafi kiwon lafiyar al’umma.
6. Hana shan taba sigari a guraren da akwai yara ko kuma ake kula da yara, ko ilimantar da mutane ko kula da kiwon lafiya. Sauran guraren da abun ya shafa sun hada da guraren cin abinci, guraren nishadi da wasan yara, tashar motoci, guraren kallon wasanni, da sauran su.
7. Za a hukunta duk wani mamallakin ko mai kula da wuraren da aka ambato a lamba 6 wanda yaki hani ko ya bari aka sha taba sigari a gurin da ke karkashin ikon sa 8. Hana yin tallar sigari ta kowace kafa ko siga
9. Tabbatar da ingancin taba sigarin da ake sayarwa, kamar yadda aka kayyade.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie