Ci Gaba Da Yakin Biafra, Wacce Iriyar kudun Muwa Amurka Da Israela Suka Bawa Nigeria.
YAKIN BIAFARA PART 4
Daga : Hamisu_Hassan_Ahmed
Yakin Biafara,yaki ne da akai asarar rayuka masu yawa, amma har yanzu wasu suna kokarin a maima ta shi.
tun daga da, har zuwa yanzu zakaga Larabawa ne da yan Afurka turawa sukafi samun cinikin makai awurin su,saboda sune sukafi kisan junan su saboda wata karamar manufa.
kasashen yamma su baruwan su da mutuwar miliyoyin jamaa matukar bukatar su tana biya, amma su bazasu taba yarda akai musu wani hadari kasar su ba.
Idan mukaci gaba da maganar yakin Biafara da kasashen da suka bada gudun mawa za muga:
Amurka: tace: tana karfafa Nigeria a zahiri saboda sunce:bazasui jayaiya da Ingila ba akan arzikin da take kwasa a Nigeria.kasan wani lokaci siyasar su tana tafiya saboda daga karshe kowa zai samu raban shi.
ammafa idan muka duba magana ta boye zamuga Amurka suna tare da yan tawaye saboda: Gowon yanemi makamai daga wurin su suka hana,har yace:shiba taimako yake nema ba yanada kudin siya amma suka hana asiyar mai.dama ita siyasar Amurka haka ta gada,wato zata tsaya akowane bangare,to duk wanda yai nasara zasuce nasu ne, duk da munsan shugaban Amurka Nixon yakira kowane bangare akan sulhu ammafa yana karfafa Biafara aboye.
wato arzikin da turawadai suka gani awancan lokacin yasa sun rikici har kowa na neman yanda zai mallake shi takowace hanya.
Kasar Israila: ta dade tanason ta samu karfi a Nigeria, wanda haka yai wahala musamman zamanin Tafawa balewa.awani labari da naga ni yanacewa:ministan kassr Iraila yataba haduwa da Tafawa balewa awurin wani taro sai yace masa:inaso muhada dangantaka da Nigeria mai kyau, sannan inaso kabar karfafa larabawa akan fadan mu da falastin,sai tafawa Balewa yamai nuni da bindigar da ke tare da mai tsaron lafiyar shi yace:wannan itace mafita akan mulkin mallakar da kukeyi,wato zamu taimaka wurin fitar da ku.
sai mintan yace:irinka bai dace yajagoranci wannan kasa ba,aiko baayi wata daya ba saiga mummunan juyin mulki da kisan Tafawa balewa da Sardauna wanda wannan dalilin shi yakara haifar da yakin Basasar Biafara.
wato akwai kasashen da zasu sa akashe musu ko waye saboda bukatar su tabiya.
shiyasa zakaga ton shekara ta 1966 Ojukwu yafara neman makamai daga wurin su,wato tun kan afara yaki,amma alokacin yakin tai dubara, wato shine taba Nigeria yan wasu makamai a 1968 domin badda kama.amma duk yawancin man dake zuwa daga Ivory Coast zuwa Biafara nasu ne, da kuma makan dake zuwa da sunan abinci.shiyasa kake ganin wannan Kanun yana rataya kayan su da kuma kirkiro asalin karya domin sucigaba da taimakon ballewar dayake nema ayau.
Soviet union wato Rasha ayan zu.
ita ada tafara karkata zuwaga Biafara, amma tunda Nigeria ta hada Alakar kasuwanci da su musamman bude kafadin motoci, sai sukace sun gane Nigeria tanason hadin kan kasa ne.kuma kasan ita Rasha tafi muamala da Gwamnati fiyeda yantawaye amafi yawan lokaci.
Ivory Coast: Felix ,wato shugaban wannan kasa, wanda yazamu hadari akan cigabn Afurka,fransa tai amfani dashi wurin tabbatar da maida Afurka karkashin su. wannan mutum dashi akashirya juyin mulkin Gana na mai kishin Afurka wato Nkkrumah.sanan ana zargin sa wurin juyin mulkin Thomas sankara shima mai kishin Afurka.sannan ga yadda kasar shi tazama wurin rabama yan tawaye makamai zuwa Biafara.
-Cahadi ,Sudan ,sunba Nigeria gudun mawa da gaske.
Wato dai wani yakin duniya ne akaso ashirya domin mutane su kashe kan su wasu kuma sui amafani da arzkin su.
irin su Gabon,Zimbabiwe, da su Afurka ta kudu,da tanzania yawan ci zakaga sun karfafa ne saboda karkashin kasashen da ke juya su.
abun mamaki har yanzu bamu dau darasi daga tarhi ba, saboda har yanzu abun da yafaru jiya shi aketata maimatawa ayau.
har yanzu masu saidama duniya makamai sune ke hada fada akoina saboda manufar su.
yanda aka aka shirya tsarin mulkin Nigeria anyi shine don kar azauna lafiya don kuma laifi yatabata akan wata kabila.
taya aka sakama mutane mumman kabilanci kuma don me aka sa shi? Zamuji.
Shin dan Afurka akwai ranarda zai samu saukin rayuwa koko wasu zasuita amfani da shi wurin rusa kasar shi da jamar shi?
shin mutanen da suka ba yan Arewa jagoranci alokacin samun yancin kai, shin sne sukaje suna ziga sauran kabilu akan kar su yarda?
wanene suke shiryama yan Arewa gadar zare don aga kamar suke danniya tun daga da har zuwa lokacin Babangida ya hana Abiola zabenda duniya tasan shike da nasara?
saboda me wasu ke jawo rigima amma sai suje sui barcin su, su kuma talakkawa musiba ta hau kan su?
ayi hakuri yan uwa akan tsawaitawa, manufar itace mu gano bakin zaren inda aka jefa mu cikin hadari da kuma neman hanyar ficiwa daga ciki.
No comments
Post a Comment