An haramtawa wani shaihin malami yin wa'azi a Saudiyya sakamakon bayyana rashin dacewar barin mata su tuka mota, a inda ya bayyana hakan da shashanci.
A wani bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, Sheikh Sa'ad al Hajari ya ce kaifin tunanin mata rabin na maza ne, kuma da zarar sun kammala cefane idan suka je kasuwa to aikin kwalkwalwar tasu na zama rubu'in na namiji.
Daman dai ba a amince wa mata su yi tuki ba a kasar duk da cewa babu wata doka kan hakan.
Tsokacin da Sheikh Sa'ad al- Hajari ya yi kan batun haramtawa mata a Saudiyya tuka mota, ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta da muhawara.
Al Hajari ya fara ne da cewa an halicci mata da kankanuwar kwakwalwa, don haka maza suka fi su kaifin fahimta.
Bai tsaya a nan ba sai da ya kara da cewa: "Mata ba su da cikakkiyar kwakwalwa, rabi aka ba su, da zarar kuma sun kammala sayayya a manyan shaguna, rabin kwakwalwar na koma wa kwata."
Don haka ya dasa ayar tambaya, "Shin za a bar mutumin da ba shi da cikakkiyar kwakwalwa ya tuka mota?"
Martanin da mabiya shafinsa suka mayar ba mai dadi ba ne, hasali ma wasu na ganin bai kamata a matsayin da ya ke da shi na babban malamin addinin musulunci, ya yi kalami irin haka ba.
Wasu ma na ganin ya kamata ma hukumomin Saudiyya su dakatar da shi daga yi wa al'umma wa'azi ko yin Limancin Sallah.
No comments
Post a Comment