Labaran da ke zuwa mana a halin yanzu na nuni da cewa wata uwa mai suna Mercy Segun da ke da shekaru akalla 42 ta gurfana a gaban wata kotu dake a garin Abuja bisa zargin ta da akeyi da yi wa diyar ta hukuncin da ya saba ma hankali.
Ita dai matar Mercy, an maka ta kotun ne bisa tuhumar ta da akeyi da yi wa diyar ta ukuba ta hanyar sa mata tattasai a farjin ta tare kuma da muzgunamata akan laifin da bai taka kara ba balle ya karya.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun ya bayar da wadda ake tuhumar beli akan kudi Naira dubu 30 sannan kuma ya daga shari'ar har sai 25 ga watan Satumba
No comments
Post a Comment