Fitacciyar jarumar nan ta wasan kwaikwayon Hausa da turanci wato ta Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta bayyana cewa korar da aka yi mata daga masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ta daga ta zuwa mataki babba sannan kuma ta budo mata kofofi na alkairi. Jarumar wacce ta bayyana haka a wata hira da tayi da jaridar Guardian inda ta bayyana cewa duk da dai abin bai yi mata dadi ma, hakan kuma ya kara haska ta a idon duniya.
“Kawai daga na taba wani a yayin gudanar da shiri sai ace na karya doka. A tunanina koma mene kayi ai kai da ubangijin kane. Duk abinda nake yi ai ina kokarin kiyaye hakkokin addinina da kuma al’adar yankin da na fito. Saboda haka bana tunanin na cancanci hukuncin da aka yi mun a matsayin da nake. Jarumar ta bada dan takaitaccen tarihin rayuwar ta ta baya inda ta bayyana cewar ta kasance tana sha’awa tare da yin rawa tun lokacin da take a matakin karatu na primary har ya zuwa matakin karatu na sakandire. Ta kara da cewar ba’a irin kowanne film take fitowa ba inda ta bayyana cewar ta sha kin karbar roles da yawa da take ganin sun ci karo da al’adar yankin da ta fito. Daga ciki akwai inda aka taba yi mata tayin ko zata iya fitowa a matsayin yar madigo(lesbian) wanda ita taki karba don kare mutuncinta. An tambaye ta shin ko akwai bambanci a yanayin gudanar wasan kwaikwayo tsakanin Kannywood da Nollywood? Jarumar wacce ta fito a cikin wasu fina-finan Nollywood kamar su The Light Will Come, and Sons of the Caliphate. Ta bayyana cewa kusan duk tsarin daya ne sai dai yan bambance-bambance da ba’a rasa ba ta bangaren al’ada da kuma yanayin mutanen gurin da ake gudanar da harkar wasan kwaikwayon. Wannan shine dan abinda Arewamobile.com ta dan tsakuro muku daga cikin hirar da jaridar Guardian tayi da jaruma Rahama Sadau.
Arewablog
No comments
Post a Comment