Pages

Games

Wednesday, 6 September 2017

Tirka-Tirka: Ministar Buhari tayi tawaye, ta goyi bayan Atiku matsayin dan takarar ta a 2019

A cikin wani lamari mai cike da sarkakiya a siyasance, an kama ministar mata da walwalar su ta Gwamnatin Muhammadu Buhari kuma mamba a cikin majalisar zartarwa ta tarayyar Najeriya Hajiya Sanata Jummai Alhasan tana yi wa Atiku Abubakar kamfe din zama shugaban kasa a 2019.
Wannan lamari dai dake da kama da cin amana na dauke ne a cikin wani faifan bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta dauke da hoto da muryar ministar yayin wata ziyarar ban girma da ta kai masa.
Tirka-Tirka: Ministar Buhari tayi tawaye, ta goyi bayan Atiku matsayin dan takarar ta a 2019
Tirka-Tirka: Ministar Buhari tayi tawaye, ta goyi bayan Atiku matsayin dan takarar ta a 2019
Bestarewa.com.ng
 dai ta samu cewa Sanata Alhasan din kamar yadda ta fada ta jagoranci tawagar shugabannin jam'iyyar APC ne na jihar Taraba tare da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar zuwa wajen ta.
Ga dai abunda ta ta fada a cikin bidioyn a takaice: Your excellency Baban mu, shugaban kasar mu inshaAllah a 2019. A gabanka, mutanen kane, magoya bayanka har abada daga jihar Taraba. Sun zo gaisuwar bar girma, gaisuwar Sallah da kuma yi maka murna na wannan daukaka da Allah ya kara maka."
"Yanzu ga su nan, mun zo da Ciyaman din jam'iyya - shine shugaban mu saboda haka gashi nan Alhaji Garba Chedi, ga kuma Coordinator din ka.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a
Bestarewa@gmail.com

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie