A ci gaba da yaki da 'yan kungiyar Boko Haram, a yanzu haka ana samun 'yan sintiri da ke amfani da bindigogi kirar gida.
Akwai sama da 'yan sintiri dubu ashirin da biyar da ke bayar da taimako ta bangaren yaki da 'yan Boko Haram.
'Yan sintirin sun ce ba sa fargaba, kuma a shirye suke su taimaka wa al'umma.
To amma, sun koka da cewa 'yan Boko Haram na da manyan makaman yaki, yayin da su kuma bindigarsu in aka yi harbi sau daya, shi ke nan sai an sake yi ma ta duri in ji su.
Yawancin 'yan sintirin dai matasa ne masu jini a jika, kuma suna yin gadin duk hanyoyin da suke kyautata zaton 'yan kunar bakin waken Boko Haram za su bullo.
A wasu lokuta 'yan sintirin na tafiya tare da sojoji inda suke shiga lungu da sako domin farautar masu tayar da kayar bayan.
Daruruwan 'yan sintiri sun hadu da ajalinsu a irin wannan aiki, inda 'yan Boko Haram suka kashe mambobin kungiyar sintirin sama da dari shida .
To sai dai kuma duk da wannan taimako da 'yan sintirin ke yi, ana zarginsu da kwatar kudi da kuma yi wa mata fyade.
Sannan kuma ana zarginsu da kisan gilla ga mutanen da ba su ji ba su gani ba.
Abin fargaba a nan shi ne, mene ne makomar 'yan sintirin idan aka murkushe 'yan Boko Haram? domin akwai yiwuwar su zama sabuwar barazana da nuna bijirewa ga al'umma har ma ba mamaki su fi karfin hukuma.
Kwamandan kungiyar 'yan sintirin a jihar Borno, Lawan Ja'afar, ya yi gargadin cewa komai zai iya faruwa muddin baa fara daukar matakin dakile matsalar ba.
Kwamandan ya ce: " Ina kira ga gwamnati da ta samar da ayyuka ga 'yan sintiri, domin hakan ne zai ba su damar ci gaba da daukar nauyin iyalansu".
Za dai a iya fuskantar matsaloli da dama kamar fashi da makami da satar mutane domin neman kudin fansa, idan har aka kyale 'yan sintirin babu abin yi in ji kwamandan.
No comments
Post a Comment