Pages

Games

Thursday, 28 September 2017

Kun san yadda za a kauce wa kamuwa da sankarar mama?

Wannan makala ce kan bayanai game da yadda ake kamuwa da cutar sankarar mama da yadda za a iya kauce mata, kuma wannan makala an yi ta ne don amsa tambayoyinku da ku ka turowa BBC kan batun, wadanda muka yi alkawarin amsa muku.
Sankara dai tana aukuwa ne a lokacin kwayar halitta mai illa ta fara hayayyafa fiye da yadda ya kamata. Wannnan hayayyafar kwayar halittar yakan kai ga matakin ciwo mai tsanani, kuma a wasu lokutan yakan kai ga mutuwa.
Sankara dai ta kan kama mata da maza a sassa daban-daban na jikinsu.
Alkalluma daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ce sankarar mama (breast cancer) ita ce sankarar da ta fi kama mata a duniya, inda mata miliyan daya da rabi ke kamuwa da cutar a ko wacce shekara.
Har wa yau, alkaluman sun nuna cewar, ita sankarar mamar ce ta fi kashe mata da yawa a duniya.
Kuma a shekarar 2015 sankarar mamar ta yi sanadiyyar mutuwar mata 570,000 a duniya.
Dr Zainab Bagudu, likitar mata da kanana yara, kuma matar gwamnan jihar Kebbi, wadda ta kafa gidauniyar MedicAid da ke yaki da cutar sankara a arewacin Najeriya ta ce: "A Najeriya, muna da karancin samun tabbacin yawan ko wacce cuta, ko mura ko malariya, balle ciwo mai tsanani kamar sankara.
"Amman an yi kiyasin cewar mutum sama da 250,000 ne kamuwa da cutar a ko wacce shekara a Najeriyar," in ji ta.
"Diezani na fama da cutar daji"
Shan barasa yana kawo cutar daji
Ana gab da samun maganin cutar daji ta huhu
An samu karuwar cutar daji a wasu kauyukan China
Amman ta yaya ake kamuwa ta cutar sankaran mama?
Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suka aiko mana ta shafinmu na BBC Hausa.com bayan da muka bukaci su turo tambayoyin da suke so sani kan wannan batu.
Dr Zainab Bagudu ta ce cutar sankara tana da wahalar ganewa kuma ba a san takamaiman dalilin da ke sa a kamu da cutar ba.
Ita ma wata kwararriyar likita da ta taba aiki a asibitin kasa na Najeriya da ke Abuja, wadda a yanzu haka ta bude nata asibitin, Dr Hajara Yusuf, ta ce har yanzu ba a gano takamaiman dalilin da ke janyo cutar ba.
Amman ta ambato dalilai da ke taimakawa wajen kamuwa da cutar.
Dalilan sun hada da yawan shekaru (a Najeriya macen da ta kai shekaru 50 na iya kamuwa da cutar), da shan barasa, da amfani da sinadarin Estrogen da kwayoyin halittar da ke dauke da bayanai na gado wadanda ke iya haifar da cutar.
Likitar ta ce sankarar mama da ta mahaifa ne suka fi damun mata.
"Amman maruru ko kurji da ke iya fitowa kan mama ciwo ne na fata," in ji Dr Hajara.
Likitar ta bayyana cewar kurji yana jikin fata ne, bai kai ga abin da ke cikin mama ba.
Sai dai kuma ba mata kadai ne suke kamuwa da cutar sankarar mama ba, maza ma suna kamuwa da cutar.
Masana sun ce kashi daya cikin dari na masu sankarar mama maza ne.
Shima kululu ba shi da wata barazana?
Likitoci sun ce in har mace ta ji wani kululu ko wani kulli cikin nononta, ya kamata ta garzaya zuwa asibiti domin a yi maganin matsalar tun tana karama.
Sai dai kuma ba ko wanne kululu ne sankara ba. Sai an cire kululun an gwada kafin a gane cewar sankarar mama ne ko kuma ba shi ba.
Har wa yau likitoci na son macen da ta lura cewar wani nononta ya fi wani girma ta je asibiti a duba ta domin a iya dakile cutar dajin da wurwuri.
Kazalika in mace ta lura cewar kan nononta ya koma ciki ta yadda jariri ba zai iya kama kan nonon ba, ana son ta je a duba domin yana daga cikin alamomin sankarar nono.
Baya ga haka idan macen da ba ta shayarwa ta ga ruwan na fitowa daga nononta a hade da jini, ita ma ana son ta garzaya asibiti domin a duba.
Sai dai kuma ba ko wacce mace da ke da daya daga cikin wadannan alamun ne ke da ciwon ba, duk da cewa alamu ne da ke nuna cewa mace za ta iya kasancewa da sankarar mama.
Ta yaya za a guje wa Sankarar mama?
Masana sun ce za a iya guje wa sankarar mama ne ta hanyar fitar da gujewa abubuwan da ke taimaka wa sankarar mama irin su barasa da sinadarin Estrogen da sauransu.
"Da farko zan ce yana da kyau mutum ya ci abinci mai kyau. Abinci, ba wanda ake saya a kanti ko ake sarrafawa a zuba a robobi ko gwangwanaye ba, abinci wanda muke nomawa, wanda za a ci.
"Ba wanda ya yi shekara daya a cikin firiza ko kuma firji ba, ko kuma an dauko shi cikin gwangwani daga can kasashen waje, ya dade a tashar jirgin ruwa, sannan kuma a zo da su Najeriya," In ji Dr Zainab Bagudu.
Wace illa sankarar mama ke yi wa yaro? Wannan ma tambaya ce da ta fito daga wajen mutane da dama kan batun.
Masana sun ce sankarar mama ba ta yi wa jaririn da ake shayarwa illa domin shi sankarar ba ta yaduwa da jini ko nono. Saboda haka ana ganin mace mai wannan larurar za ta iya shayarwa ba tare da wani fargaba ba.
Ta yaya ake maganin sankarar mama?
Ana maganin sankarar mama ne a manyan asibitoci inda ake da kayayyakin aikin da kwararru kan maganin sankara.
Ban da maganin sha, ana maganin sanakarar mama ta hanyar cire sankarar mama ya kama da kuma gasa wurin da ya kamu da ciwon ta yadda sankarar za ta mutu.
An yi wannan makalar ne kan sankarar mama bayan masu bibiyar Sashen Hausa na BBC suka turo mana tambayoyi game da larurar.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie