Pages

Games

Tuesday, 26 September 2017

Shugabanni su tsaya su yi aiki ba zargin Gwamnatocin baya ba - Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa ya koma game da harkar Shugabanci
- Atiku yace Shugabanni su yi aiki ba su yi ta kokawa abin da ya shude ba
- Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dai ta zargi Gwamnatocin baya
Alhaji Atiku Abubakar yayi wasu maganganun da ka iya cewa da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake.
Shugabanni su tsaya su yi aiki ba zargin Gwamnatocin baya ba - Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku tare da Buhari
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan Atiku Abubakar ya caccaki irin su Shugaba Muhammadu Buhari a wasu kalamai da yayi a shafin sa na Tuwita jiya kamar yadda mu ka ji. Atiku yayi kira ga Shugabanni da su tsaya su yi aiki ba tare da daura laifin kan wasu ba.
KU KAAtiku yace Shugabanni su tsaya kurum su yi aiki ba wai a tsaya a rika zargin Gwamnatocin baya da yin ba daidai ba. Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dai ta yi ta zargin Gwamnatocin baya musamman na Goodluck Jonathan da kashe kasar.
Da alamu dai Wazirin na Adamawa Atiku Abubakar zai nemi takara a zaben 2019. Kuma a baya Atiku yayi kaca-kaca da Gwamnati mai mulki a wata hira da yayi da Gidan VOA na Amurka.

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie