Gwamnan Jihar Kaduna ya ga abin da ya sa shi kuka a yau
– Malam Nasir El-Rufai ya zubar da hawaye ne dazu a Zaria
– Hakan ya faru ne bayan ya hadu da yaron da aka cirewa idanu
Yau an ga wani bangare na Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai inda ya rusa kuka yayin da ya hadu da wani yaro da matsafa su kayi wa illa a Makarantar Yahaya Hamza da ke Zaria.
Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna yayi kuka har da hawaye yayin da ya je rabawa yara kayan aiki dazu a wata Makaranta a cikin Garin Zaria. Gwamnan ya kai ziyara ne Makarantar da yaron yake wanda aka gyara aka kuma raba wasu na’urorin karatu a Yau Laraba.
El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu" width="1200" />
El-Rufai yayi kukan ne bayan ya hadu da yaron da wasu matsafa su ka zakulewa idanu kwanakin baya mai suna Sadiq Usman wanda ke da shekaru 5 kacal a Duniya. Gwamnan ya buge da kuka a gaban Jama’a yayin da yaron ya zauna a kan cinyar sa har ta kai yana share hawaye da tsumma.
Kwanaki kun ji cewa mai girma Gwamnan Jihar Kadunan Malam Nasir El-Rufai ya kai ta’aziya ga iyalin Abidu Yazid wanda aka sace surukar sa aka yi garkuwa da ita bayan an kashe mijin ta
No comments
Post a Comment