Kamar dai yadda aka sani a kasar Najeriya, nahiyyar Afirka da ma duniya baki daya, Alhaji Aliko Dangote yana daya daga cikin mutanen da za su daga dan yatsa idan anzo maganar kudi.
Kudi wanda hausawa ke cewa masu gidan rana, su na tsonewa mutane idanu, sanadiyar hakan ne ya sanya aka bincike domin gano wadanda suka yi fice wajen tarin dukiya a sassa daban na duniya.
Shafin
Bestarewa.com.ng
ya bankado daga kididdiga ta binciken jama'a akan wadanda suka kere kowa kudi a nan Najeriya, wanda kuma ko shakka ba bu Alhaji Aliko Dangote ya kere kowa.
Bestarewa.com.ng
ya bankado daga kididdiga ta binciken jama'a akan wadanda suka kere kowa kudi a nan Najeriya, wanda kuma ko shakka ba bu Alhaji Aliko Dangote ya kere kowa.
A wata ruwaya daga maganganun al'umma sun bayyana cewa, ana yiwa Dangote mai kudin bakar fata a duk duniya domin a cewar su indai mutum baki ne to kuwa Dangote ya fi shi kudi.
Ga jerin sunayen mutane 10 na Najeriya da suka yi fice wajen tarin dukin da masana'antunsu ko kuma sana'ar su:
1. Alhaji Aliko Dangote - Mai gidauniyar Dangote
2. Mike Adenuga - Mai kamfanin Con oil da kamfanin sadarwa na Globacom
3. Femi Otedola - Mai kamfanin Forte oil
4. Orji Uzor Kalu - Mai gidauniyar Slok
5. Cosmos Maduka - Mai gidauniyar Coscharis
6. Jimoh Ibrahim - Mai kamfanin inshora na Nicon da kuma Global Fleet
7. Jim Ovia - Bankin Zenith da kamfanin sadarwa na Visafone
8. Pascal Dozie - Kamfanin sadarwa na MTN da bankin Diamond9. Oba Otudeko - Gidauniyar Honeywell, kamfanin mai na Pivotal da kamfanin sadarwa na Airtel
10. Alhaji Sayyu Dantata - Gidauniyar mai na MRS
No comments
Post a Comment