Babban Dan wasan nan Ronaldo na shirin yin aure
– Ronaldo zai auri Budurwar sa Georgina Rodriguez
– A shekara mai zuwa ne ‘Dan wasan zai zama Ango
Ana dai sa rai babban Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya shiga daga ciki a badi kamar yadda labari yake zuwa mana.
Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure" class="article-image__picture" height="640" src="https://i.onthe.io/vllkyt6d6e62tlbcf.afcc316d.jpg" style="border: 0px; display: block; height: auto; margin: 0px auto; max-width: 100%; padding: 0px;" title=
"Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure" width="960" />
Tauraron Dan wasan na Real Madrid Cristiano Ronaldo zai auri budurwar sa Georgina Rodriguez a shekara mai zuwa ko da dai har yau ba a san takamamen ranar ba. Yanzu haka dai Rodriguez mai shekaru 23 ta na da cikin ‘dan Ronaldo.
KU KARANTA: An kama wasu da ke yaudarar mata a Turai
Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure" class="article-image__picture" height="492" src="https://i.onthe.io/vllkyt7tc9b9413qv.c4d2bf41.jpg" style="border: 0px; display: block; height: auto; margin: 0px auto; max-width: 100%; padding: 0px;" title="Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure" width="820" />
Jaridar Correio de Manha tace Dan wasan dai ya ba Budurwar ta sa zobe mai tsada har na fam miliyan Euro £232,000 wanda ya kai kusan Naira Miliyan 100. Kwanan nan ne aka ga Rodriguez ta shiga Makarantar koyon rawa a Sifen.
Ronaldo ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve kwanakin baya, haka kuma dama dai yana da yaro mai shekaru 6 a Duniya. Ko da yake dai har yanzu Dan wasan bai tabbatar da ainihin iyayen yaran ba.
No comments
Post a Comment