Jaruma Saratu Gidado wadda akafi sani da Daso, ta zanta da Mujalla Fim ta wannan watan inda aka tattauna da ita akan abinda ya shafi sana'arta da kuma aurenta. A Zantawar ne ta bayyanawa duniya cewa ita har yanzu matar aure ce kuma ma'akaciya. Kuma takara da cewa kamar yanda sauran matan aure suke tinkaho da su masu aurene to ita haka take yin tutiya da cewa itama matar aure ce kuma ma'aikaciya. Majiyarmu dai ta samu cewa a baya bayan nan dai anata cece-kuce akan cewa auren Daso ya mutu. Amma Jaruma Saratu Gidado ta musanta haka inda tace har yanzu ita matar aurece kuma suna zaune da mijinta lafiya.
Aikin da take yi baya haifar mata da wata matsala agidan mijinta. Sannan ta shelantawa duniya cewa har yanzu tana yin hausa fim, duk da tana da aurenta. haka bai hanata fitowa amatsayin da ya dace da itaba, amatsayinta na matar aure. Daga karshe tayi fatan alkairi ga masoyanta da kuma masarautar kano wadda Sanusu Lamido II yake milki.
No comments
Post a Comment